Amurka ta ƙaryata iƙirarin Iran kan ƙwace tankar mai

Amurka ta musanta iƙirarin da Iran ta yi cewa, dakarunta na musamman sun daƙile yunƙurin ƙwace mata wani jirgin ruwan ɗaukar ɗanyen mai a tekun Oman da Amurkar ta yi.

Jami’an Amurka da suka yi magana bisa sharaɗin a sakaya sunayensu, sun ce babu ƙamshin gaskiya a rahoton na Iran, saboda Amurka ba ta yi yunƙurin ƙwace tankar dakon man Jamhuriyar Musuluncin ba.

Sun ƙara da cewa, gaskiyar lamari shi ne, dakarun Iran ne suka karɓe wani jirgin ruwan dakon man Ƙasar Vietnam a watan da ya gabata, kuma abin da sojin ruwan Amurka ke yi tun daga wancan lokaci shi ne sintirin sanya ido a kan halin da ake ciki.

A makon da ya gabata ne, Iran ta yi iƙirarin cewa dakarunta na musamman sun daƙile wani yunkuri daga sojin ruwan Amurka na ƙwace mata wata tankar dakon manta maƙare da danyen mai a tekun Oman.

Zaman tankiya na ci gaba da ƙaruwa tsakanin Tehran da Washington a yayin da aka samu tsaiko a tattaunawar farfaɗo da yarjejeniyar nukiliyar Iran ta shekarar 2015, kuma a Larabar nan babban jami’in tsaron ƙasar Ali Shamkhani ya ce, yarjejeniyar za ta wargaje matsawar shugaba Joe Biden bai bada tabbacin Amurka ba za ta sava alƙawari ba.