INEC ta tabbatar da batun sace akwatin zaɓe a wasu rumfuna a zaɓen Anambara

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Rahotanni sun bayyana cewa, kwamishinan hukumar zaɓe na INEC a Jihar Anambra, Nwachukwu Orji, ya tabbatar da rahotannin tarzoma da sace-sacen akwatunan zaɓe a wasu rumfunan zaɓe a Jihar.

Ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a gidan Talabijin na Channels a yau Asabar.

Orji ya ce, an samu rahotannin sace akwatin zaɓe a wasu rumfunan zaɓe a ƙaramar hukumar Idemili.

Hukumar ta ce, ’yan daba sun yi awon gaba da akwatunan zaɓe sama da bakwai ɗauke da ɗaruruwan ƙuri’un zaɓe.

A cewarsa, “akwai matsalar sace ƙuri’a a lokacin zaɓen. Wasu ’yan daba ne suka zo suka kawo cikas, suka kwashe akwatunan zaɓe. Hakan ya faru ne a Idemili Arewa da Kudu, inda aka yi awon gaba da kimanin akwatunan zaɓe bakwai.”

Orji ya kuma ce, akwai wuraren da aka hana jami’an INEC shiga, lamarin da ya kawo tsaikon gudanar da zaɓen. Sai dai ya ce ba zai ɗauki hakan a matsayin babban ƙalubalen tsaro ba.

Ya qara da cewa, “ba zan yi la’akari da shi a matsayin babban ƙalubalen tsaro ba saboda zaɓen ya kasance cikin kwanciyar hankali. Abin mamaki ne ga mutane da yawa kasance cikin kwanciyar hankali duba da barazanar tsoro na kai hare-hare.”

Da aka tambaye shi ko za a soke ƙuri’u a yankunan da abin ya shafa, ya ce, “wannan shawara ce da za a yanke daga baya amma a yanzu dole ne a kammala aikin.”