Daga AMINA XU
A shekaru 50 da suka gabata, tsohon shugaban ƙasar Amurka Richard Milhous Nixon, ya kai ziyarar aiki a ƙasar Sin, matakin da ya nuna cewa, hulɗar ƙasashen biyu ta kama hanyar da ta dace.
Yayin ziyarar, ɓangarorin biyu sun kai ga cimma matsaya ɗaya, game da ƙara bunƙasa hulɗar dake tsakaninsu wadda ta dace da moriyar ƙasa da ƙasa, da kuma buƙatar kauce wa yin babakare a yankin Asiya-Pacific.
To sai dai kuma shugaban Amurka mai ci Joseph Robinette Biden, ya kira ƙasar Sin a matsayin “ƙalubale”, har ma ya fake da batun Taiwan don tada rikici a tekun Pacific. Jim kaɗan bayan ya ɗare kujerar shugaban ƙasa, Biden ya tava bayyana cewa: Amurka ta dawo, to amma ina ta dawo?
Mai zane: Amina Xu