Maza da yawa ba sa son a riƙa kwarzanta mata – Zainab Julde

“Mata na fuskantar ƙalubalen haɗa aikin gida da na ofis”

Daga ABUBAKAR A. BOLARI, a Gombe

Honorabul Hajiya Zainab Adamu Julde ita ce Sarauniyar Sudan ta Akko, ƙwararriyar malamar makaranta ce, kuma ‘yar kasuwar da ta yi gwagwarmayar rayuwa da har ta taɓa zama Kwamishinar Ma’aikatar Mata da Walwalarsu ta Jihar Gombe. A yanzu haka kuma ita ce Shugabar Mata ta Yankin Arewa maso Gabas ta Jam’iyyar PDP. A zantawar ta da sashen Mata A Yau na Shafin Gimbiya na jaridar Manhaja, ta bayyana irin gwagwarmayar da ta yi a rayuwa har takai matsayin da ta ke a yanzu:

MANHAJA: Ko wacce ce Zainab Julde?
HAJIYA ZAINAB: TO, sunana Hajiya Zainab Adamu Julde, ni Bafulatana ce, kuma Batangaliya, domin mahaifiyata Batangaliya ce, mahaifina kuma Bafulatani. An haifeni ne a garin Kumo fadar hedkwatar Ƙaramar Hukumar Akko a Jihar Gombe. A nan na girma, iyayena suka sani a makarantar firamare ta ‘Central’ da ke garin Kumo. Bayan na gama, na ta fi sakandaren Arabiya ta mata da ke garin Alkaleri a Jihar Bauchi, wato ‘Women Arabic Teachers Collage’ wacce yanzu ta zama ‘Government Girls Arabic secondary school’. Ina kammala wa, sai aka min aure a shekarar 1989. 

Bayan nan, sai na tafi Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Gwamnatin Tarayya da ke garin Bauchi, ‘Federal polytechnic’ Bauchi inda na karanta sha’anin kasuwanci wato ‘Diploma in Marketing’ a tsakanin shekara ta 2006 zuwa 2008. Daga nan, sai na tafi jami’ar nan ta karatu daga gida ‘Open University’ NOUN, na karanta sha’anin kwantar da tarzoma, wato ‘Peace and Conflicts resolution’ a tsangayar su da ke Bauchi. 

Ko Hajiya ta yi aikin gwamnati?
Eh. Na fara aiki a matsayin malamar makaranta, inda na koyar a makarantar firamare ta ‘central’ da ke garin Kumo. Bayan wani lokaci, sai na koma Hukumar Tattara Kuɗaɗen shiga, ‘Board of Internal Revenue’ da ke garin Kano, ina nan bayan wani lokaci sai aka mayar da ni sashin kula da harkar lafiya matakin farko ta aramar Hukumar Fagge a jihar ta Kano, wato ‘primary health care department’, a nan ne na ajiye aiki, na ci gaba da harkokin kasuwancina gadan-gadan, da ma a lokacin da na ke aiki ma Ina kasuwanci a ɓangaren sayar da abinci, wato ‘restaurant’, mai suna Daɗin-Kowa a garin Bauchi. Ina kula da gidan abinci na ne sai tsohon gwamnan Jihar Gombe Alhaji Ibrahim Hassan Dankwambo Talban Gombe, ya ɗauko ni, ya ba ni kwamishinar harkokin mata, amma kafin ba ni kwamishinar ta mata, na riƙe muƙamin P.A ta mai taimaka wa gwamnan, kana daga bisani ya mayar da ni SSA, ‘senior special Assistant’ ɗin sa, ma’ana, babbar mai taimaka wa gwamna ta musamman.

Ko akwai wata nasara da ki ka samu?
Na samu nasara sosai matuƙa, domin a dalilin kasuwancin da na yi da kuma aikin gwamnatin da na yi ne, na ke iya ciyar da jama’a har ma da ‘yan’uwana a ɓangarorin rayuwa daban-daban, kuma alhamdu lillah, babbar nasarar ma ita ce, gidan abincina da yanzu haka na ke da ma’aikata kimanin hamsin da suke aiki a wajen.

Kin fuskanci wani ƙalubale?
Mata a har kullum suna fuskantar ƙalubale, musamman wajen haɗa aikin gida da na ofis, ga kuma kula da maigida da sauran ɗawainiya a wajen aiki. Kuma duk ƙoƙarin mace wasu mazajen ba su so a ce mace ta yi ƙwazo alhali su suna wajen, hakan ta sa na fuskanci ‘yan ƙalubale kaɗan, amma dai ban ɗauki irin hakan a matsayin ƙalubale ba, domin hakan ne ke ƙara wa mace himma, har ta yi fice a cikin maza.

Kin taɓa halartar wani kwas na musamman?
Eh. Na yi kwas ɗin Difloma a vangaren kwamfuta, na yi kwas na ‘Trauma healing’ a Jos kan warware matsalolin tashe-tashen hankula.

Mene ne burinki a rayuwa?
Burina a rayuwa shi ne, na ga cewa, ina taimaka wa ‘yan’uwana mata ta vangaren karatu da kiwon lafiya, musamman waɗanda suke yankunan karkara, waɗanda ba su da ƙarfi.

Wanne irin tufafi ya fi burge ki?
To batun tufafi gaskiya na fi son na ɗaura Atamfa, zani da riga, na yafa gyale, na yi fita irin ta mutunci, kowa ya ganni, ya ganni da qimata ta kamala da kamun kai. 

Ko ki na zuwa wani wurin don yin hutu? 
Ba na zuwa hutu ko’ina. A lokacin hutu ina yin sa ne a tsakanin iyalaina daga garin Kumo zuwa Gombe, zuwa Bauchi, saboda na fi son zama cikin ‘yan’uwana, domin zan fi shaƙuwa da su, na san matsalolinsu. 

Ki na cikin wasu ƙungiyoyi?
Ni mamba ce a ƙungiyar ‘National Institute Management’ NIM, sannan shugabar ƙungiyar mata a tsarin shugabanci ‘women in leadership’.

Kin taɓa zuwa wata ƙasa?
Na je ƙasashe irin Saudi-arebiya, na je Indiya da Dubai da wasu ƙasashe a Afirka.

Ya batun iyali?
Alhamdu lillah. ‘Ya’yana huɗu. Mata uku, namiji ɗaya.

Ko ki na da wata shawara ga iyaye?
A matsayina ta uwa, ina mai bai wa iyaye shawarar cewa, idan sun gane karatun ‘ya mace alheri ne, to su ba su dama su yi, domin idan mace ta yi karatu, ko wajen zaman gidan aurenta zai banbanta da na wacce ba ta yi ilimi ba, saboda idan aka ilmintar da ‘ya mace ilimin addini da na zamani, rayuwarta za ta inganta matuƙa, sannan kuma bana goyon bayan yi wa yarinya auren wuri, a hanata karatu, ko da sakandare ne balle kuma masu ɗaura wa ‘ya’yansu talla. Waɗannan iyayen kamar sun bai wa ‘ya’yan lasisi ne na lalacewa.

Madalla. Mun gode.
Ni ma na gode ƙwarai.