Amurka ta nesanta kanta da harin Isra’ila kan cibiyar gas ɗin Iran

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban Amurka Donald Trump ya fito fili ya nesanta ƙasarsa daga harin sama da Isra’ila ta kai kan babbar cibiyar iskar gas ta Iran wato filin South Pars, yana mai cewa Amurka ba ta da hannu a lamarin.

A wata sanarwa da aka fitar ta bakin Fadar Shugaban ƙasa ta White House ta hanyar shafin ɗ da kuma manhajar Truth Social, Trump ya bayyana cewa Isra’ila ta kai harin ne cikin fushi sakamakon abubuwan da ke faruwa a yankin Gabas ta Tsakiya.

Ya jaddada cewa Amurka ba ta da masaniya game da harin, tare da ƙara da cewa ƙasar ƙatar ma ba ta da hannu ko labari kan lamarin.

Sai dai ya ce rashin wannan bayani ya sa Iran ta kai harin ramuwar gayya kan wasu cibiyoyin gas na ƙatar, lamarin da ya haifar da asara da gobara mai yawa.

Trump ya yi gargaɗin cewa Isra’ila ba za ta sake kai wani hari kan filin South Pars ba, sai dai idan Iran ta sake kai hari kan ƙatar. Ya kuma ce idan hakan ta faru, Amurka za ta mayar da martani mai tsanani, ko da kuwa ba tare da amincewar Isra’ila ba.

Kamfanin ƙatarEnergy ya tabbatar da cewa an kai hare-hare da makamai masu linzami kan cibiyoyin gas a Ras Laffan, wanda ya jawo gobara mai ƙarfi da babbar ɓarna.

Tun kafin harin, an kwashe ma’aikata daga wurin bayan Iran ta yi barazanar kai hari a matsayin martani ga hare-haren da aka kai kan filin South Pars.

Baya ga ƙatar, rahotanni sun nuna cewa Iran ta kuma kai hari kan wasu matatun mai a Saudiyya da kuma cibiyar gas ta Habshan a Abu Dhabi, lamarin da ya tilasta United Arab Emirates rufe cibiyar.

Masana tattalin arziki sun ce wannan rikici ya fara haifar da tashin farashin makamashi a duniya, inda farashin mai da iskar gas ke ƙaruwa sakamakon fargabar tangarɗar samar da kayayyaki.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu wata sanarwa kai tsaye daga Isra’ila ko Iran dangane da kalaman Trump.

By ukarofi