Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Jami’an tsaro sun daƙile wani yunƙurin sace ɗalibai a Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnati (Government Girls’ College) da ke jihar Bauchi kamar yadda jaridar TheCable ta wallafa.
Wani rahoto daga jaridar Zagazola Makama, wadda ke mayar da hankali kan batutuwan yaƙi da ta’addanci a yankin Tafkin Chadi, ya ce lamarin ya faru da misalin ƙarfe 4 na asubahin ranar Lahadi, 15 ga Maris.
Rahoton ya bayyana cewa wasu mutane da ba a san ko su wanene ba sun yi ƙoƙarin shiga harabar makarantar ta wani ɓangare na katangar makarantar da ke kusa da gidajen ma’aikata.
An ce masu gadin makarantar da ke bakin aiki sun gano motsin mutanen tare da sanar da jami’an sintiri na tsaro, waɗanda suka garzaya wurin cikin gaggawa.
Bisa ga rahoton, waɗanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun tsere daga wurin bayan sun hango jami’an tsaron na tunkarowa.
Rahoton ya ƙara da cewa lamarin ya haifar da ɗan firgici a cikin makarantar yayin da ɗalibai suka fara yin ihu a cikin harabar makarantar, amma babu wata ɗaliba da aka sace ko aka ji wa rauni.
Jami’an tsaro sun ce an shawo kan lamarin, kuma an ƙara tsaurara sintiri da sa ido a kewayen makarantar domin hana sake faruwar makamancin wannan barazana.
Haka kuma, hukumomi sun ce ana ci gaba da bincike domin gano waɗanda suka aikata yunƙurin harin tare da cafke su.
