An ƙaddamar da bayar da rigakafin zazzaɓin cizon sauro a Kebbi

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Gwamantin jihar Kebbi ta ƙaddamar da bayar da maganin rigakafin zazzaɓin cizon sauro ga ƙananan yara daga shekara ɗaya zuwa biyar.
An ƙaddamar wannan shirin da haɗin gwiwa tsakanin ƙungiyar lafiya ta Malaria Consortium da gwamantin jihar Kebbi ƙarƙashin hukumar lafiya ta jihar Kebbi.
Da ya ke jawabi a fadar mai martaba Sarkin Kabin Argungu Alhaji Sama’ila Muhammad Mera, Gwamna Malam Nasir Idris ya bayyana cewa yana da kyau mutane su yi amfani da wannan damar su kai yaran su da ba su wuce shekara biyar ba domin a yi musu rigakafin.
Sarkin Kabin Argungu Alhaji Sama’ila Muhammad Mera ya nuna jin daɗin sa bisa ga yadda gwamnati ta ke amfani da wannan masarautar a duk lokacin da wani abin alkhairi ya samu.
Ya kuma yi kira ga al’umma da su bayar da goyon baya don ganin an sami nasara a cikin wannan shirin. Kada su hana a yi wa ƴaƴan su wannan rigakafin saboda cutar zazzaɓin cizon sauro ba ƙaramar illa ta ke yi ba musamman idan aka yi la’akari da alƙalumman masana harkokin lafiya.

By ukarofi

Leave a Reply