
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
An ƙaddamar da shirin dasa bishiyoyi guda 22,000 a sassan jihohin Kano da Jigawa a wani yanayi da bunƙasa lamuran kula da muhalli domin walwalar al’umma.
Kwalejin Tarayya ta Ƙere-ƙeren kayan Fasahar Noma da ke Kano tare da haɗin-gwiwar gwamnatin jihar Kano, Gidauniyar British American Tabaco Nigeria Foundation da kamfanin Ahalson Nigeria Limited da masu harkar samar da iri da kayan gona sune suka haɗu don ƙaddamar da wannan shiri.
Wannan dai wani wani yunƙuri ne na rage tsananin zafin rana da ake fama da shi a sassan faɗin jihohin.
A wata hira da manema labarai, Shugaban Ahalson General Enterprises, Ahmed Ali ya ce wannan shiri ne da suka zaɓi ƙananan hukumomi guda 11 – huɗu a Jigawa sai kuma bakwai a Kano domin dasa waɗannan bishiyoyi.
Ya bayyana cewa, an samar da tsarin yadda za’a kula da waɗannan bishiyoyi har zuwa girmansu wanda in har aka cimma nasara kan haka, to za’a magance gurɓacewar muhalli da kwararowar Hamada har ma da ƙarancin ruwan sama da ake fama da shi.
Wakilin Jihar Kano a taron, Abdul Ladan Ajuma wanda kuma ya wakilci kwamishinan ma’aikatar tsare-tsare da kasafin kuɗin jihar, ya ce sun ɗauki matakin haɗin-gwiwar ne kasancewar Kano tana daga cikin gurare masu tsananin zafin rana gami da ƙalubalen sare bishiyoyi da ake fama da shi a fadin jihar har ma da maƙotanta.
Ya bayyana cewa, “tun asali gwamnati tana da wannan ƙudiri sai kuma gashi an samu wata ƙungiya ta ƙasa-da-ƙasa ta kawo tallafi ta hannun wannan makaranta da haɗin-gwiwar kamfanin Ahalson sai muka hadu da su muka yi tsare-tsare.”
Ya ƙara da cewa, an riga an tsara yadda za’a samar da masu kula da su har zuwa girmansu. A yanzu, shirin zai fara ne da ƙananan hukumomin Ɗambatta, Makoɗa da Dawkin-Kudu.

