An ƙaddamar da Manhajar WikiHausa a birnin Kano

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

A ranar Asabar da ta gabata, an ƙaddamar da babbar Manhajar nan ta Hausa mai suna WikiHausa da take ƙunshe da rayuwar Bahaushe a harshen Hausa.

Isah Uba Chamo wanda shi ne shugaban Manhajar kuma shi ne ya samar da ita, ya bayyana cewa an ƙirƙiri Manhajar ne domin ta samar da ingantaccen ilimi a yanar Gizo.

Ya ce aƙalla shekara 6 da kafa wikiHausa, amma ya ce da ya yawa wasu ba su san shi ne ya kirƙire ta ba, wasu sun ɗauka ‘yan ƙasar waje ne suka yi ta.

Ya kara da cewa” WikiHausa Manhaja ce da muka ƙirƙira domin samar da kowane irin ilimi cikin Harshen Hausa a yanar gizo wanda take kiyaye al’ ada da addinin malam bahaushe”

“Kuma ta ƙunshi komai domin muna da marubuta 1800 daga faɗin duniya, duk abinda aka turo mana za mu duba mu gyara sannan mu ɗora duniya ta gani.

Ba iya Nijeriya ba ne ake sauraronmu ba, sama da ƙasashe 20 suna bibiyarmu a duniya. Muna da mabiya da yawa a duniya” a cewar Isah Chamo

Tunda farko a jawabinsa babban jigo a tafiyar Farfesa Abdallah Uba Adamu ya bayyana cewa
WikiHausa tana magana akan duk wani abu ingantaccen na Bahaushe, ko da Hausa aka yi ko da larabci aka yi ko da Turanci aka yi in dai ya yi magana akan Hausa WikiHausa za ta saka Shi.

Ya ƙara da cewa “WikiHausa ba tana nufin harshe Hausa ba kawai, aa ana maganar alu’mmar Hausawa da kuma rayuwar Hausawa baki daya’

‘A baya turawa suna zuwa bincike-bincikensu akan Hausawa, amma da matsalar boko Haram ta zo sai suka tsorata suka daina zuwa , to daina zuwan su sai ya ba mu kwarin gwiwa, domin da suka daina zuwa sai mu zame masu hanyar da za mu rika ba su bayananmu,

“Domin mu abinda muke so shi ne sa da ɗan chaina ya zo ya yi bincike akan Kasuwar Kantin Kwari, ƙwara mu je mu kai masu, wannan shi ne muhimmancin WikiHausa, kuma InshaAllahu ba mu fara don mu daina ba, duk da yake yan’uwanmu ba sa so, amma muna da yara zarata kuma zafafa da suke taimaka mana, mu gyara Shi ta yadda za a yi amfani da shi a duniya” inji Farfesa Abdallah

By ukarofi