Dikko Raɗɗa ya kafa kwamitin sabon albashi na N70.000 a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamna Dikko Raɗɗa ya amince da kafa kwamitin da zai tsara yada gwamnati zata fara biyan ma’aikatan jihar sabon tsarin albashi.

Wata takardar sanarwa daga ofishin mataimakin gwamna ɗauke da sa hannun Hassan Abubakar Ɗayyabu na nuna cewa sakataren gwamnatin jihar Abdullahi Garba faskari zai kasance shugaban kwamitin.

Sauran mambobin kwamitin sun haɗa shugaban ma’aikatan jihar da Kwamishinonin kasafin kuɗi da na ma’aikatar kudi da kuma na ƙananan hukumomi da masarautu.

Akwai kuma babban akawun kuɗi na jihar da shugaban hukumar tattara haraji na jihar da daraktoci masu binciken kuɗi na jiha dana ƙananan hukumomi.

Sai kungiyar ƙwadago ta ƙasa reshen jihar da shugaban ƙungiyar ma’aikatan ƙananan hukumomi tare da na ƙungiyar manyan ma’aikatan gwamnatin jihar .

Sai babban sakatare a ofishin sashin kula da yan fansho ƙarƙashin ofishin shugaban ma’aikata .

A ranar juma’a mai zuwa ake sa ran mataimakin gwamnan jihar Faruk Lawal Joɓe zai ƙardamar da kwamitin a ofishin sa ,kamar yadda sanarwar ta bayyana.

By ukarofi