Ministan tsaro ya ziyarci Zamfara, ya yaba da ƙoƙarin Gwamna Lawal wajen yaƙi da ‘yan bindiga

Spread the love

zDaga USMAN KAROFI

Ministan Tsaro, Mohammed Badaru, ya yaba wa Gwamna Dauda Lawal kan jajircewarsa da goyon baya ga ayyukan soji a Jihar Zamfara.

A ranar Alhamis, ministan ya ziyarci fadar gwamnatin Zamfara da hedikwatar Rmrundunar haɗin gwiwa ta Arewa Maso Yamma, (Operation Fansar Yamma) da ke Gusau.

Cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, an bayyana cewa ziyarar tana da nufin ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin jiha da ma’aikatar tsaro.

Sanarwar ta ƙara da cewa ministan ya tattauna batutuwan da suka shafi tsaro a matsayin ci gaba daga ziyarar da gwamnonin Lawal na Zamfara da Raɗɗa na Katsina suka kai Ma’aikatar Tsaro a makon nan.

A jawabinsa, Gwamna Lawal ya sake nanata ƙudirin gwamnatinsa na yin aiki tare da dukkan hukumomin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya a Zamfara.

“Ina so in gode wa Ministan Tsaro bisa wannan ziyara da ya kawo domin tattauna batutuwan tsaro a Zamfara.

“Kwanan nan, ni da Gwamnan Katsina mun ziyarci ofishin ministan a Ma’aikatar Tsaro inda muka tattauna kan wasu manyan matsaloli.

“Kamar yadda kuke gani, bayan kwanaki biyu ministan ya zo mana ziyarar aiki. Wannan abin a yaba ne kuma yana nuna jajircewar ministan.

“Zamfara na fuskantar ƙalubale masu yawa na tsaro, amma a matsayina na gwamnati mai alhakin kare rayukan mutane, muna bukatar neman taimako da haɗin kai. Mun ƙuduri aniyar bai wa sojoji dukkan goyon baya da suke buƙata.

“Muna kai wannan yaki ga ‘yan bindiga domin ba za mu cigaba da kare kai kawai ba. Abin da na gani ya nuna cewa batun ‘yan bindiga zai zama tarihi, Insha Allah.

“Na yi alƙawurra ga Ministan. Haka nan, na sayi manyan motoci guda goma na tsaro da aka yi wa kariya don taimaka wa sojoji. Sauran kayan aiki suna nan za a basu domin taimaka musu wajen yaƙi da ‘yan bindiga.

“Idan muka iya magance matsalar ‘yan bindiga a Zamfara, za mu samu saukin kashi 90% na matsalar tsaro.

“Ina rokon sojojin, musamman rundunar soji, cewa muna buƙatar su. Na tabbata suna da dukkan abin da ake buƙata domin kawo ƙarshen wannan yaki.

“Ina tare da ku kuma na ƙuduri aniyar kare mutanen Zamfara. Ina godiya ga Minista musamman bisa wannan lokaci da ya dauka domin kasancewa tare da mu.”

A jawabinsa, Ministan Tsaro, Alhaji Badaru Abubakar, ya yaba wa gwamnatin Gwamna Lawal kan irin tallafin da ta ke bai wa sojojin domin samun nasarar aikin yaƙi da ‘yan bindiga a Zamfara.

“Muna fara ganin cigaba, godiya ga goyon bayan mai girma Gwamnan Jihar Zamfara, wanda ya samar da wuraren zama ga dakarun tsaro, kayan aiki, na’urorin ɗaukar hoto daga nesa, motocin aiki da kuma mai. Har ma ya bai wa dakarun manyan motocin yaƙi. Wannan goyon baya da ya bayar ne ya sa muke samun ci gaba a wannan yaki. Mai girma Gwamna, muna godiya gare ka.”

By ukarofi