Tinubu ya tsuke wa ministocinsa bakin aljihu

Spread the love

Ya umarci su su yi amfani da motoci uku a tawagarsu

Ya bayyana haƙiƙanin dalilin korar wasu ministoci

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya taƙaita yawan motocin da ministocinsa da sauran shugabannin hukumomin gwamnati ke amfani da su a tawagarsu zuwa guda uku, inda ya ce ba za a ƙara wa kowa ba.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnatin, Mista Bayo Onanuga, ya fitar, Shugaba Tinubu ya ce, wannan wani mataki na daga cikin matakan da gwamnatinsa ke ɗauka ne na rage kashe kuɗaɗen gwamnati.

Sanarwar ta ce Shugaba Tinubu ya kuma bai wa ministocin nasa da shugabannin hukumomi da ka da su yi amfani da masu kare lafiyarsu ko jami’an tsaro da suka wuce biyar, inda kuma ya umarci mai bai wa shugaban shawara kan tsaron ƙasa domin tattaunawa da sojoji da ‘yan sanda da sauran masu ɗamara kan yadda za a rage yawan jami’an tsaron.

“An sanar da matakin rage kuɗin ne a yau a cikin wata sanarwa da shugaban ƙasa ya sanyawa hannu. “A watan Janairun wannan shekara, Shugaba Tinubu ya ɗauki muhimman matakai domin rage yawan kuɗaɗen da gwamnati ke kashewa, ta hanyar rage rakiyar tawagarsa zuwa ƙasashen waje daga 50 zuwa 20. Don tafiye-tafiye na cikin gida, ya rage shi zuwa jami’ai 25.

“Hakazalika ya rage tawagar mataimakin shugaban ƙasar zuwa jami’ai biyar a tafiye-tafiyen ƙasashen waje da 15 na tafiye-tafiyen cikin gida.

“A cikin umarnin da ya bayar a yau, Shugaba Tinubu ya kuma umurci dukkan ministoci, da shugabannin hukumomi da su sanya jami’an tsaro aƙalla biyar su kasance tare da su.

“Tawagar tsaron za ta ƙunshi ‘yan sanda huɗu da jami’in DSS guda ɗaya,” in ji sanarwar.

Da ma dai ko a watan Janairu sai da shugaban ya ce ya ɗauki matakan rage kashe kuɗaɗen inda ya rage yawan ‘yan tawagarsa yayin bulaguro ƙasar waje daga 50 zuwa 20 sannan shi kuma mataimakin shugaban ƙasa aka bar masa mutum biyar.

Dalilin Tinubu na kori ministoci biyar – Fadar Shugaban ƙasa:

Bayo Onanuga, mai ba Shugaban ƙasa Bola Tinubu shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, ya bayyana dalilin da ya sa aka kori wasu ministoci, wanda ya ce ya samo asali ne daga ƙididdigar ‘yan Nijeriya da kuma hujjoji masu inganci.

Ya kuma bayyana rawar da mai bai wa shugaban ƙasa shawara ta musamman kan harkokin siyasa Hadiza Bala Usman ta taka wajen korar ministocin daga majalisar.

A ranar Laraba ne Tinubu ya sauke Barr. Uju-Ken Ohanenye, tsohuwar ministar harkokin mata, Lola Ade-John, takwaransa na ma’aikatar yawon buɗe ido, Farfesa Tahir Mamman (SAN) wanda ya jagoranci ma’aikatar ilimi, Abdullahi Muhammad Gwarzo, ƙaramin ministan gidaje da raya birane da Dr. Jamila Bio Ibrahim, a baya ministar ci gaban matasa na muƙamansu.

Matakin da shugaban ya ɗauka ya kawo ƙarshen cece-kuce na tsawon makonni da kuma yin murabus ɗin da ya karu bayan dawowarsa daga Faransa a ƙarshen hutunsa.

A wata hira da aka yi da shi a gidan Talabijin na ARISE, Onanuga ya ce Tinubu ya yi aiki da tunanin ‘yan Nijeriya.

A cewarsa, Bala Usman an sanya ta ne don sa ido kan aikin tantancewa, wanda ya haɗa da tattara ra’ayoyin jama’a kan ayyukan ministocin.

Mai taimaka wa shugaban ƙasar ya ƙara kare matakin da Tinubu ya ɗauka na naɗa sabbin ministoci bakwai a majalisar ministocinsa.

Ya ce gwamnatin Nijeriya na buƙatar hannu sosai don shawo kan matsalar da ƙasar ke fuskanta.

Ya ce, “Lokacin da aka rantsar da ministoci, a gaskiya shugaban ƙasar ya gaya musu cewa a matsayinsa na shugaban ƙasa yana da ikon ɗaukar aiki da kora, kuma ba zai yi ƙasa a gwiwa ba wajen sauke ministocin da ba za su iya yin aiki ba.

“Akwai garambawul a watan Oktoban shekarar da ta gabata inda kuma ya sake maimaita irin wannan gargaɗin game da shirinsa na yin ƙoƙarin yi wa majalisar ministocin sa a koda yaushe idan har wasu ba su taka rawar gani ba.

“Ba wani abu ne kawai aka yi shi cikin jin daɗi ba, ina ganin Hadiza Bala Usman, mai ba da shawara ta musamman kan harkokin siyasa da haɗin kai a gaskiya ta kawo fasaha a cikin ta ta hanyar neman jin ra’ayin ‘yan Nijeriya. Don haka, duk wanda aka cire an yi shi ne bisa wasu hujjoji masu ma’ana da kuma fahimtarsu da jama’a. ’Yan Nijeriya a zahiri sun yi nasara kuma shugaban ya yi aiki da sakamakon.”

Onanuga ya ƙara da cewa korar ba wai yana nufin ministocin ba su cimma burin Tinubu ba.

“Amma tsammanin jama’a. Makonni da suka gabata a taron majalisar ministocin, shugaban ƙasar ya ƙalubalanci ministocin da su fito su shaida wa ‘yan Nijeriya abin da suka yi a tsawon shekara ɗaya ko fiye da haka.

“A cewar shugaban ƙasar, tunanin da mutane ke yi a waje shine cewa mutane suna jin cewa gwamnati ba ta aiki, kuma gwamnati ta yi imanin cewa gwamnati na yin aiki, amma ministocin ba su fita don aiwatar da gwamnati yadda ya kamata ba,” inji shi.

By ukarofi