
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Tarayya ta sanar da ɗage jana’izar fitaccen ɗankasuwar nan, Alhaji Aminu Ɗantata, wanda ya rasu a ranar Asabar a ƙasar Hadaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE).
Ministan Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris ya shaida wa BBC batun, idna ya ce hakan ya samu ne a sakamakon rashin isar gawar marigayin akan lokaci zuwa birnin Madina.
”Akwai ƙa’idoji da gwamnatin Saudiyya ta shimfiɗa kan yadda za a shigar da gawa domin yi mata jana’iza a ƙasar, to yanzu haka ana nan ana ta cike-ciken takardu tsakanin gwamnatin Saudiyya da iyalan mamacin,”in ji ministan.
Ya kuma ce, tuni ofishin jakadancin Nijeriya a Saudiyya da iyalan mamacin suka kammala shirye-shiryen jana’izar.
Bayanai sun ce Alhaji Aminu Ɗantata ne ya bar wasiyyar binne shi a birnin Madina, inda kuma ƴan’uwansa suka nemi amincewar hukumomin Saudiyya game da buƙatar, suka kuma amince da ita, kamar yadda BBCHausa ta ruwaito.
A safiyar yau ne tawagogin gwamnatoci a matakin ƙasa da Jihar Kano suka tafi Saudiyya da nufin halartar jana’izar da aka shiryi yi a yau Litinin.
