
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Litinin ne
wasu fusatattun matasa a garin Lafiagi dake Ƙaramar Hukumar Edu ta Jihar Kwara suak karaɗe tituna, inda suka gudanar da zanga-zanga kan ƙamari da rashin tsaro ya yi a yankunansu, lamarin da ya haɗa da ta’addanci, garkuwa da mutane da kuma kashe-kashe.
A wani faifan bidiyo an ga yadda suke ɗaga allunan ɗauke saƙonnin da ke nuna suan da buƙatar ɗauki na gaggawa kan zubar da jini da ake yi da garkuwa da mutane da ya zama ruwan dare a yankunan.
Blueprint ta ruwaito cewa, matasan Irate sun banka wa ofishin Hukumar Hana sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) wuta a Lafiagi da lalata Fadar Sarkin garin inda suka yi wa sassan ginin dameji.
Kawo yanzu Hukumar ƴan sanda ba ta fitar wani saƙo game da al’amarin ba, saidai ta baza jami’ai yankin domin dawo da kwanciyar da lumanar al’umma, kamar yadda wasu muryoyi suka bayyana.
