Gwamnonin Kano da Jigawa da sarakuna sun tafi Madina jana’izar Marigayi Aminu Ɗantata

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Wasu manyan jiga-jigan ‘yan siyasa da masu riƙe da sarautun gargajiya daga jihohin Kano da Jigawa sun isa birnin Madina na Saudiyya domin halartar jana’izar Marigayi Alhaji Aminu Alhassan Ɗantata, fitaccen ɗan kasuwa kuma dattijo a Najeriya.

Tawagar ta haɗa da Gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf da Gwamnan Jigawa, Umar Namadi. Haka zalika, tsohon Gwamnan Jigawa, Barista Ali Sa’ad Birnin Kudu, da Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II, na cikin tawagar.

Sauran sun haɗa da Galadiman Kano, Matawallen Kano, Sarkin Yaƙin Kano, Injiniya Sagir Koƙi, Kwamared Nastura Ashir Sharif, Alhaji Sabiu Bako da daraktan yaɗa labarai na Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa.

Kazalika tawagar ta bayyana zuwanta a matsayin karramawa da girmamawa ga marigayin wanda ya shafe rayuwarsa yana hidima ga al’umma ta fannoni da dama, ciki har da kasuwanci, ilimi da aikin jin ƙai.

By ukarofi