Shekara 80 da suka gabata a makamanciyar wannan rana, an rattaɓa hannu kan yarjejeniya ta Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) a San Francisco, inda aka sauya tsari na yaki da duniya ta fuskanta shekaru da dama zuwa samar da kyakkyawar makoma. Tsawon shekaru 80, MDD ta tsaya a matsayin mai bayyana fatanmu na haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa, mai bayyana ma’anar burinmu na kawo ƙarshen “cutarwa a yaƙi.” A cikin wannan duniyar da ke cike da son zuciya, wannan muhimmin mataki ne da ya dace a dauka.
MDD ta kasance ƙungiya ɗaya tilo da bata da tamka, kuma ita kadai ce ta dawwama. Wannan tsayin daka yana da ban mamaki idan muka yi la’akari da yanayin kafuwarta.
Babu wata ƙungiya da za a ce ba ta da aibi. Amma domin a bayyana ƙoƙarin Sakatare-Janar ɗinta na biyu, Dag Hammarskjöld: An kafa MDD ba don ɗaukaka ɗan Adam ba sai don cetonmu daga mawuyacin hali, kuma ba za ta gaza a kan wannan manufa ba.
Muna sane da wuraren da ake yaƙi masu taɓa zuciya: Gaza, Sudan, Ukraine da sauran wurare. Rikicin baya-bayan nan tsakanin Iran da Isra’ila, wani abin tunatarwa ne ga raunin zaman lafiya musamman a yankin Gabas ta Tsakiya mai fama da tashe-tashen hankula.
Duk da haka, a cikin wannan tashin hankali, mun yi nasarar daƙile yaƙin duniya na uku. A wannan zamani na nukiliya, wannan nasara ce da ba za mu taɓa ɗauka da wasa ba. Ita ce wacce ta kamata mu kiyaye da ƙarfin ƙoƙarinmu.
A cikin shekaru 80 da suka gabata, yawancin ci gaban ɗan Adam shi ma yana da tasiri a MDD kai tsaye. Yi la’akari da nasarar da aka samu ta ci gaban ƙarni, wanda ƙasashe mambobi 189 suka karɓa a cikin ƙasashe 2000 da ƙari.
Fiye da ƙungiyoyi ƙasa da ƙasa 20 ne suka ba duniya taswirar hanya daya domin ɗaukar mataki.
A 2015, idan aka kwatanta da 1990, matsanancin talauci ya ragu sama da rabi. Mutuwar yara ta ragu da kusan kashi 50 cikin ɗari. Kuma miliyoyin yara musamman ‘yan matan da ake dannewa haƙƙi sun shiga makaranta a karon farko.
Akwai wani muhimmin labarin ci gaba, wanda ba a mantawa da shi, shi ne wargaza daula. Shekaru 80 da suka gabata, mulkin mallaka ya yi shuhura a duniya. A yau, fiye da 80 da aka yi musu mulkin mallaka a faɗin Asiya, Afirka, Caribbean, da Pacific sun sami ‘yancin kai kuma sun shiga MDD. Wannan canji da wannan Ƙungiya ta goyi baya kuma ta halatta shi ya sake fasalin tsarin duniya.
Shiga tsakani domin samar da ci gaba
Duniya ta canza sosai tun daga 1945. A yau, ƙungiyar na fuskantar matsalar ƙarancin kuɗi. Duk da alƙawarin da aka yi na 2030 don samar da ci gaba mai ɗorewa, ci gaban kuma bai daidaita ba. Daidaiton jinsi ya kuɓuce mana. Alƙawarin da muka yi na taƙaita hauhawar ɗumamar duniya da kare duniyarmu ya ƙaranta.
Waɗannan koma baya ba sun haifar da raguwar buri amma su ne manyan ƙudurorinmu. Majalisar Ɗinkin Duniya na nuna kimarta a lokutan rikici. Waɗanda suka kafa ta sun shaida ɗan Adam a matsayin mafi ɓarna kuma ba su yanke ƙauna ba, saboda ƙarfin hali. Dole ne mu zayyana Waɗannan nasarori.
Yayin da muke bikin wannan zagayowa, dole ne mu sake farfaɗo da kiran haɗin kai da aka yi daga San Francisco shekaru 80 da suka gabata.
Mun gina tsarin duniya farat ɗaya, domin rushe tsarin yaƙi. Mun yi hakan ne da hangen nesa cikin gaggawa. Yanzu kuma, mun sami kanmu a lokacin sakamako. Haɗarin yana da yawa. Haka zalika kuma ƙarfinmu na yin aiki na da yawa.
