
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rahotanni sun nuna cewa, Shugaba Bola Tinubu yana shirin dawo da dakataccen gwamnan Ribas, Siminalayi Fubara da tawagar ƴan Majalisar Dokokin jihar a wannan watan na Yuli.
Hakan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan Tinubu ya jaogranci sulhunta tsakanin gwamnan da Ministan Abuja Nyesom Wike, bisa rikicinsu na tsawon lokaci.
A watan Maris ne aka tsayar da rikicin siyasar jihar a yayin da Shugaba Tinubu ya sanya dokar ta-ɓaci a jihar tare da dakatar da Fubara, mataimakiyarsa da ƴan majalisar na tsawon watanni shida, inda ya kafa hujja da matsalolin tsaro da ya shafi satar mai daga mayaƙa a jihar mai albarkatun mai.
Tun a watan Oktoban 2023 ne rikicin ya samo asali, a lokacin da aka samu saɓani tsakanin Wike da Fubara yaronsa a siyasa kan gudanar tsare-tsaren siyasar jihar, lamarin da ya yi sanadin ƴan majalisa 27 na ɓangaren Wike suka nemi tsige Fubara.
A ƙarshen watan ne Tinubu ya nemi sulhunta ɓangarorin biyu a Fadar Shugaban Ƙasa, saidai bai a cimma nasara ba kasancewar yarjejeniyar da aka ƙulla ta rushe jim-kaɗan bayan zaman.
Haka kuma, a farkon shekarar 2024 ne Babbar Kotun Jihar Ribas ta bada umarnin barin ƴan majalisa guda huɗu na ɓangaren Fubara gudanar da harkokin majalisar dokoki da hana ƴan ɓangaren Wike tsoma baki a ciki, lamarin da ya yi sanadin ƙara hura wutar rikicin siyasar.
Duba da ci-gaba da aka samu wajen sulhunta su a ƴan kwanakin nan, ana ganin Gwamna Fubara da ƴan majalisar ka iya koma wa riƙe muƙamansu.
