Da Ɗumi-Ɗumi: APC ta ayyana 24 ga Yuli a matsayin ranar zaman NEC don maye gurbin Ganduje

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A yayin zaman Kwamitin Ayyuka na Ƙasa (NWC) na APC ne aka zaɓi 24 ga watan Yuli a matsayin ranar da za gudanar da zaman Majalisar Zartarwar (NEC) jam’iyyar domin naɗa sabon shugaban jam’iyya.

A ranar Juma’a ne Abdullahi Umar Ganduje ya yi murabus daga shugabancin jam’iyyar, lamarin da ya sa mataimakinsa na Arewa, Bukar Dalori ya karɓi kujerar na riƙon ƙwarya.

Bayan taron gaggawa na NWC’n ne a yayin ganawa da manema labarai, Mataimakin Sakataren jam’iyyar, Barista Festus Fuanter ya ce zaman zai bada damar naɗa sabon shugaba.

Ya kuma ce, tuni aka miƙa saƙon gudanar da zaman na NEC ga Hukumar Zaɓe (INEC) domin tabbatarwa.

By Babaji