Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Majalisar dokokin jihar Katsina ta buƙaci ma’aikatu da hukumomin gwamnati da kasafin kuɗin su ya ƙunshi shirye-shiryen inganta samar da abinci mai gina jiki, da su riƙa aiki tare da sabon kwamitin majalisar da aka kafa domin kula da harkokin abinci mai gina jiki.
Shugaban kwamitin kasafin kuɗi na majalisar, Hon. Lawal Yaro, ya bayyana hakan ne yayin da ma’aikatar lafiya da hukumomin da ke ƙarƙashinta suka bayyana gaban kwamitin domin kare ƙiyasin kasafin kuɗin shekarar 2027.
Hon. Lawal ya bayyana damuwa kan yadda a wasu lokuta ake samun sauye-sauye a tsare-tsare da manufofin gwamnati, amma ma’aikatu da hukumomi ba sa isar da cikakken bayani ga jama’a kan irin ci gaban da aka samu.
Ya buƙaci hukumomin da abin ya shafa su ƙara inganta hanyar sadarwa da jama’a domin su fahimci ayyukan da gwamnati ke aiwatarwa da kuma yadda ake amfani da kuɗaɗen da aka ware.
A yayin zaman, kwamishinan lafiya na jihar, Hon Musa Adamu Funtua, ya jagoranci jami’an ma’aikatar da hukumomin da ke ƙarƙashinta wajen kare ƙiyasin kasafin kuɗinsu na shekarar 2027.
Kwamishinan ya gabatar da ƙiyasin sama da Naira biliyan 30.5 domin manyan ayyukan ma’aikatar a shekarar 2027.
Haka kuma, shugaban hukumar yaƙi da cututtukan da ke rage garkuwar jiki ta Jihar Katsina, Dr. Bala Nuhu Kankia, ya kare ƙiyasin sama da Naira miliyan 70 domin gudanar da ayyukan hukumar a shekarar 2027.
Da yake duba yadda ake gudanar da aikin kare ƙiyasin kasafin kuɗin, Kakakin Majalisar, Rt. Hon. Nasir Yahaya Daura, ya bayyana gamsuwarsa da yadda ma’aikatu da hukumomin gwamnati ke ba majalisar haɗin kai.
Ya yi kira da a ci gaba da wannan haɗin gwiwa domin ƙarfafa kyakkyawar dangantakar aiki tsakanin majalisar dokoki da ɓangaren zartarwa.
