An buƙaci Fulani su zama masu haɗin kai da neman zaman lafiya a Legas

Spread the love

Daga BALA KUKKURU a Legas

Sarkin Fulanin ƙaramar Hukumar Badagiry da ke Jihar Legas, Alhaji Umar Mohammed Bello, ya buƙaci al’ummar Fulanin yankin Badagiri da kewayenta gabaɗaya da su zama masu haɗin kai da junansu tare da neman zaman lafiya a garin na Badagiry da kewayenta bakiɗaya.

Sarkin Fulanin, wanda ya kasance ɗan asalin jihar Neja da ke yankin arewacin Nijeriya, mazaunin garin Badagiri ta Jihar legas, ya buƙaci hakan ne a ranar Lahadin da ta gabata a lokacin da yake gabatar da jawabinsa na taron bikin wankan sarautarsa ta sarkin Fulanin Badagiry da kewayenta gabaɗaya.

Taron bikin wankan sarautar ya samu halartar sarkin Fulanin Jihar Legas Alhaji mohammed Abubakar Bambado na biyu wanda ya samu wakilcin sarakunan fadar masarautar Fulanin jihar da sarakunan Fulanin jihohin yankin Yarabawan wanda suka hɗda da jihar Ogun, Oyo, Ond, Osun, Ekiti da sauran waɗansu da suka fito da jihohin arewacin Nijeriya dama na aasashen da suke yi makwabtaka da Nijeriya bakiɗaya. 

Taron ya gudana ne a harabar fadar sarkin Fulanin na garin Badagiry da ke cikin jihar Legas. 

Tun da farkon buɗe taro da addu’a, waɗansu daga cikin sarakunan Fulanin dama su yi tsokaci a wajan taron bikin wankan sarautar, inda suka gabatar da muhimman jawabai ɗaya bayan ɗaya. 

A ciki jawaban nasu hadda kiraye-kiraye na neman haɗin kawunan junan su da kuma ba juna shawarwari ta yadda za su ƙara ƙoƙari a wajen sanya ‘ya’yayansu makarantun boko dama na a Arabiyya bakiɗaya.

Sun jinjina wa Gwamnatin jihar Legas a ƙarƙashin jagorancin Gwamnan jihar Baba Jide Sanwo Olu bisa ga ƙoƙarinsa na kawo ayyukan cigaban jihar tare da haɗa kawunan al’ummar jihar domin su cigaba da samun zaman lafiya a Legas da kewayenta gabaɗaya.

Shima a nasa tsokacin a wurin taron bikin wankan sarautar tasa ta sarkin Fulanin ƙaramar hukumar Badagiry da kewayenta, Alhaji Umar Mohammed Bello bayan ya kammala yi wa taro sallama irin ta addinin Musulunci, sannan kuma ya cigaba da nuna jin daɗinsa dangane da yadda ya ga ɗimbin al’ummar Fulani da Hausawa da sauran ƙabilun waɗanda suka zo taya shi murnar gabatar da wannan taro. 

Akan haka ya cigaba da yi wa Allah ubangiji godiya da ya ba shi damar gabatar da wannan taro tare da yi wa al’umma fatan alheri na komawar su gidajen su lafiya.

Hakazalika, ya cigaba da ƙara yin kira ga al’ummar Fulanin mazauna ƙaramar hukumar Badagiry dasu zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya, domin yin magana da harshe ɗaya idan hakan ta taso.

A ƙarshe, ya yi wa Nijeriya addu’a tare da fatan alheri na ƙara samun cigaba da zaman lafiya mai ma’ana.

By ukarofi