Daga JAMEEL GULMA a Kebbi
Sakataren ƙungiyar Miyetti Allah kuma mataimaki na musamman ga Mataimakin Gwamnan Jihar Neja, Alhaji Bello S. Fulani, ya nemi al’ummar Fulani makiyaya da ke zaune a yankin ƙaramar hukumar Mokwa a Jihar Neja su nemi wuraren zama na dindindin, don cin moriyar dimukraɗiyya.
Ya yi wannan kiran ne a ofishinsa da ke garin Mokwa ranar Talatar da ta gabata. Bello Fulani ya bayyana cewa, wannan gwamnatin ta Jihar Neja a ƙarƙashin jagorancin Umar Bago a shirye ta ke ta samar da ilmi ga Fulani makiyaya a rugarsu. Saboda haka a maimakon yau suna nan gobe suna can, yana da kyau su nemi wuraren zamana dindindin, inda zai zama mallakarsu da za su iya gina gidaje, yana mai cewa, ta haka ne kawai ayyukan ci gaba za su iya kai wa wajensu.
Ya kuma nemi al’ummar Fulanin su guji duk wani abu da ke iya kawo tashin hankali tsakanin makiyaya da ’yan kasuwa da manoma.
Ya bayyana cewa, tun lokacin da suka karɓi ragamar jagorancin wannan ƙungiyar, kawo yanzu an sami nasarori sosai a ɓangaren zamantakewa tun kama daga al’ummar yankin zuwa sarakuna, musamman Sarkin Mokwa Ndalele, wanda yanzu haka an kama hanyar fitar da duk inda wani burtali ya ke tun kama daga na tarayya zuwa na jihohi zuwa ƙananan hukumomi ya zuwa wuraren shan ruwan dabbobi.
Sai dai ya koka kan yadda waɗansu masu kunnen ƙashi daga cikin makiyaya ke tsallakawa zuwa yankunan waɗansu ƙananan hukumomi da ke maƙotaka da Mokwa da suka haɗa Mashegu da Laɓun suna samun matsaloli da ’yan bijilanti da manoma, inda ya ja hankalinsu da su daina wuce iyakar. Idan kuma sun tsallaka, to, don Allah su riƙa bin ƙa’idojin mutanen da suka shiga yankunansu.
Ya kuma bayar da tabbacin wannan ƙungiyar za ta ci gaba da bayar da gudunmawa, don samun cigaba mai ɗorewa a wannan yankin tare da ɗaukar duk matakin da ya kamata ga kangarrun ’ya’yanta, don samun zaman lafiya.
