Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Ƙungiyar SERAP mai fafutukar yaƙi da cin hanci da rashawa a Nijeriya, ta buƙaci Shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya binciki yadda gwamnonin jihohi 36 da Birnin Tarayya Abuja suka yi amfani da bashin da suka karɓo daga Bankin Duniya.
Ƙungiya ta buƙaci Tinubu ya umarci Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi (SAN) da hukumomin da ke yaƙi da cin hanci da rashawa da su gaggauta bincikar yadda aka kashe bashin na dala biliyan 1.5.
Gwamnonin sun ciyo bashin ne domin rage raɗaɗin talauci da ƙara inganta jin daɗin al’umma a faɗin jihohinsu.
Buƙatar bincikar gwamnonin da SERAP ta yi na ƙunshe ne a cikin wata wasiƙa mai ɗauke da sa hannun mataimakin daraktanta, Kolawale Oluwadare, wacce ta sanya a shafinta na yanar gizo.
SERAP ta kuma buƙaci Tinubu da ya umurci Fagbemi da hukumomin da ke yaƙi da cin hanci da rashawa da su gaggauta bincikar zargin karkatar da bashin dala biliyan 3.121 da Gwamnatin Tarayya ta karɓo daga Chana.
“Akwai rahotannin da ke nuna cewa bashin dala biliyan 1.5 da Bankin Funiya ya ba jihohi 36 da Abuja da bashin $3.1bn da gwamnatin tarayya ta samu daga China, an karkatar da su ko ba a san yadda aka yi da su ba.”
“Bincike tare da tuhumar zargin cin hanci kan karkatar da bashin Bankin Duniya da na Chana, zai yi daidai da Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya.”
“Mun fahimci cewa yayin da gwamna yake da kariya daga kamu ko tuhuma, ba ya da kariya daga bincike. Duk wani zargin aikata laifi kan gwamna mai ci za a iya bincike a kansa har zuwa lokacin da zai sauka sannan ya rasa kariya.”
“Abubuwan da aka gano kan wannan binciken, za su iya zama silar fara shirin tsige wannan gwamnan,” inji Kolawale Oluwadare.
ƙungiyar ta ba shugaba Tinubu wa’adin kwana bakwai domin ɗaukar matakin da ya dace, inda ta yi barazanar ɗaukar matakin shari’a idan bai yi wani abu a kai ba
