An buɗe babban taron wakilan JKS karo na 20

Daga CMG HAUSA

An buɗe babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta ƙasar Sin JKS karo na 20, da misalin ƙarfe 10 na safiyar yau Lahadi a Beijing, fadar mulkin ƙasar Sin.

Wakilan jam’iyyar, gami da waɗanda aka ba su goron gayyata na musamman sama da 2300 sun halarci taron, tare da wasu da ba ’yan jam’iyyar kwaminis din ba da sauransu. Za kuma a rufe taron a ranar 22 ga wata.

A wajen taron, za a saurara, gami da duba rahoton aiki na kwamitin ƙolin JKS na 19, da duba rahoton aikin da kwamitin ladabtarwa na kwamitin ƙoli na JKS na 19 ya gabatar.

Kana, za a amince da gyararren shiri na kundin ƙa’idojin jam’iyyar JKS, da kuma zabar membobin kwamitin kolin jam’iyyar da na kwamitin ladabtarwar jam’iyyar a sabon zagaye.

Jam’iyyar kwaminis ta ƙasar Sin mai tarihin shekaru 101, ta shafe tsawon shekaru 73 tana kan karagar mulkin ƙasar Sin, wato tun kafuwar Jamhuriyar Jama’ar ƙasar Sin.

Babban taron wakilan jam’iyyar, gami da kwamitin kolinta, su ne hukumar koli ta jam’iyyar.

A kan gudanar da babban taron wakilan jam’iyyar a duk bayan shekaru biyar.

A wajen taron, shugaba Xi Jinping ya gabatar da muhimmin rahoto, a madadin kwamitin ƙolin jam’iyyar na 19.

Xi ya ce, a shekaru 10 da suka gabata, yawan GDPn ƙasar Sin ya ƙaru daga kuɗin Sin Yuan tiriliyan 54, har zuwa tiriliyan 114, kana jimillar tattalin arzikin ƙasar Sin ta ɗauki kaso 18.5 bisa ɗari, na jimillar tattalin arzikin duk duniya, adadin da ya ƙaru da kaso 7.2 bisa ɗari, wanda ya sa ƙasar ta zama ta biyu a duniya.

Shugaba Xi ya kuma ce, ƙasar Sin ta zama babbar aminiyar cinikayya ga ƙasashe da yankuna sama da 140, kuma jimillar kuɗin cinikayyar kayayyaki ta ƙasar tana kan gaba a duniya, kana, yawan jarin waje da ƙasar Sin ta jawo, da yawan jarin da ta zuba a sauran ƙasashe duk suna kan gaba.

A halin yanzu ƙasar Sin tana haɓaka bude kofarta ga ƙasashen waje a fannoni daban-daban.

Xi ya ƙara da cewa, ƙasar Sin ta samu babban ci gaba wajen raya wasu muhimman fasahohi, da ƙara bunƙasa sabbin sana’o’i da dama, ciki har da zirga-zirgar kumbuna masu ɗauke da dan Adam a sararin samaniya, da binciken duniyar wata da duniyar Mars, da binciken yankin ruwan teku mai zurfi, da nazarin manyan na’urori masu ƙwaƙwalwa, da taurarin ɗan Adam, da amfani da makamashin nukiliya don samar da wutar lantarki, da ƙera manyan jiragen sama, da harhada magunguna da sauransu, al’amarin da ya sa Sin ta shiga jerin ƙasashen dake kan gaba a duniya, wajen yin ƙirƙire-ƙirƙire.

Har wa yau, shugaba Xi ya nuna cewa, ya dace ƙasar Sin ta raya ingantaccen tsarin tattalin arziki irin na kasuwa mai salon gurguzu, da tsayawa gami da kyautata babban tsarin tattalin arziki irin na gurguzu, da ƙara haɓaka tattalin arziki irin na gwamnati, da kuma ƙarfafa gwiwa da jagorantar ayyukan raya tattalin arzikin da ba na gwamnati ba, ta yadda kasuwannin ƙasar za su ƙara taka muhimmiyar rawa wajen daidaita albarkatu, kuma gwamnatin ƙasar ita ma za ta kara taka rawarta.

Xi ya jaddada cewa, ya dace a raya tsarin sana’o’i irin na zamani, da maida hankali sosai kan raya sassan da suka shafi hada-hadar kuɗaɗe kai-tsaye, da raya sabbin masana’antu, da gaggauta gina ƙasar Sin mai karfin yin ƙere-ƙere, mai ƙarfin binciken sararin samaniya, mai ƙarfin zirga-zirgar ababen hawa, mai ƙarfin amfani da yanar gizo ta intanet, mai ƙarfin fasahar sadarwar zamani da sauransu.

Har wa yau, ya kamata a nuna azama wajen farfaɗo da yankunan karkara daga dukkan fannoni, da nuna fifiko wajen samar da ci gaban ayyukan noma da yankunan karkara, da ƙara saurin raya ƙasar Sin mai ƙarfin aikin noma.

Shugaba Xi ya ƙara da cewa, ana buƙatar a ci gaba da haɓaka buɗe ƙofar ƙasar Sin ga ƙasashen ƙetare, da gagguta raya ƙasar mai ƙarfin harkokin kasuwanci, da taimakawa ci gaban aiwatar da shawarar “ziri ɗaya da hanya ɗaya”, a wani kokari na kiyaye tsarin tattalin arzikin duniya, da hulɗar tattalin arziki, da kasuwanci dake ƙunshe da ɓangarori daban-daban.

Mai fassara: Murtala Zhang