An rantsar da sabon Gwamnan Ekiti

Daga BASHIR ISAH

An rantsa da Abiodun Oyebanji a matsayin sabon Gwamnan Jihar Ekiti wanda hakan ya kawo ƙarshen gwamnatin Kayode Fayemi a jihar.

A ranar Lahadi Alƙalin Alƙalan Jihar Ekiti, Mai Shari’a Oyewole Adeyeye ya rantsar da Oyebanji da mataimakiyarsa, Misis Monisade Afuye inda za su ci gaba da riƙe ragamar mulkin jihar nan da shekaru huɗu masu zuwa.

Taron rantsarwar ya samu mahalarta daga nesa da kusa, ciki har da Gwamna Rotimi Akeredolu da Gwamna Gboyega Oyetola na Jihar Osun da tsohon Gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose da sauran baƙi masu yawan gaske.

Oyebanji, wanda kafin wannan lokaci shi ne tsohon Sakataren Gwamnatin Ekiti, ya samu nasarar zama gwamna ne bayan da ya lashe zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 18 ga Yuni, 2022 a ƙarƙashin Jam’iyyar APC.

Yayin zaɓen, Oyebanji ya samu ƙuri’u 187,057 inda ya doke abokin takararsa na Jam’iyyar SDP, Segun Oni wanda ya tashi da ƙuri’u 82,211.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *