Xi ya yi bayani kan muhimman nasarori uku da aka cimma cikin shekaru 10 da suka gabata

Daga CMG HAUSA

Shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ya bayyana a yau Lahadi cewa, cikin shekaru 10 da suka gabata, an samu wasu manyan nasarori 3 masu matukar muhimmanci, wandada suka shiga tarihin JKS da al’ummar ƙasar.

Xi Jinping ya bayyana yayin buɗe babban taron mambobin JKS karo na 20 cewa, “Mun cika shekaru 100 da kafuwar JKS, gami da mun shiga wani sabon zamani na gurguzu mai sigar ƙasar Sin, kuma mun fatattaki ƙangin talauci baki ɗaya, kana mun kammala ginin al’umma mai matsakaicin ci gaba ta kowanne ɓangare, wato dai, mun cika burinmu na farko a lokacin da muke murnar cika shekaru 100 da kafuwar JKS.”

A cewarsa, waɗannan muhimman nasarori ne da suka shiga tarihi, nasarorin da JKS da al’ummar Sinawa suka yi namijin ƙoƙarin cimmawa cikin haɗin kai, kuma nasarorin da za su kasance cikin tarihin ƙasar har abada, waɗanda kuma za su yi gagarumin tasiri ga duniya.

Baya ga haka, shugaban ƙasar Xi Jinping ya yi kira ga dukkan mambobin JKS da su himmantu cikin haɗin kai, wajen tabbatar da gina ƙasar Sin mai tsarin gurguzu ta zamani ta kowacce fuska.

Xi Jinping ya ce taron ya zo ne a lokaci mai muhimmanci, kasancewar jam’iyyar da ɗaukacin Sinawa daga dukkan ƙabilu, na kan wata sabuwar hanya ta gina ƙasar zuwa ta zamani mai bin tsarin gurguzu ta kowacce fuska, da kuma ƙoƙarin cimma buri na biyu lokacin da za a yi murnar cika shekaru 100 da kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin.

Taken taron shi ne, daukaka tsarin gurguzu mai sigar ƙasar Sin da aiwatar da tunanin gurguzu mai sigar ƙasar Sin a sabon zamani da ci gaba da ɗauka babban ruhin da jam’iyyar ta kafu a kai da kasancewa cikin ƙwarin gwiwa da ƙarin ƙarfi, da ɗauka muhimman ka’idojin jam’iyyar da samun sabbin nasarori da ci gaba da tabbatar da ƙarfi da kuzarinta da himmantuwa cikin haɗin kai wajen gina ƙasa ta zamani mai bin tsarin gurguzu ta kowacce fuska, tare da kara farfaɗo da ƙasar ta kowanne ɓangare.

Cikin rahoton da ya gabatar a yayin bikin buɗe babban taron, shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, ya kuma ce JKS za ta aiwatar da dukkanin manuofi da za su ba da damar warware batun yankin Taiwan a sabon zamani, tare da tabbatar da cimma burin ɗinkewar sassan ƙasa.

Shugaba Xi ya ce warware batun Taiwan harka ce ta ƙasar Sin, wadda ya zama wajibi Sin din ta magance ta. Ya ce “Za mu ci gaba da yin aiki tukuru, domin warware wannan batu cikin lumana bisa gaskiya da kwazon aiki, amma ba za mu alƙawarta kore yiwuwar amfani da ƙarfi ba, kana muna da nufin duba yiwuwar ɗaukar dukkanin matakai.

Ya kamata masu ƙoƙarin tsoma baki na waje, da kuma masu burin ɓallewar yankin Taiwan da dukkanin ayyukansu su san haka. Ban ambaci hakan domin ’yan uwan mu na Taiwan ba”.

Ban da wannan kuma, shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, ya bayyana yayin bude taron mambobin JKS karo na 20 a yau Lahadi cewa, ƙasarsa ba za ta taba neman yi wa ƙasashen duniya babakere ko faɗaɗa iko da yankunanta ba.

A cewarsa, ƙasar Sin ta tsaya ne tsayin daka, wajen adawa da duk wani nau’i na babakere da neman iko da yaƙin cacar baka da tsoma baki cikin harkokin gidan ƙasashe da kuma nuna fuska biyu.

Masu fassara: Saminu Alhassan da Fa’iza Mustapha