Zan kawo ƙarshen matsalar tsaro a bana – Buhari

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya tabbatar wa ’yan Nijeriya cewa zai miƙa wa shugabanni masu zuwa a 2023 ƙasar ba gara ba zago, inda ya tabbatar da cewa, gwamnatinsa za ta kawar da duk wani nau’in ta’addanci.

Shugaban Ƙasar a ranar Talata, 11 ga Oktoba, 2022, ya bayar da tabbacin ne a taron Bayar da Lambar Yabo ta Ƙasa na shekarar 2022 da aka gudanar a ɗakin taro na ƙasa da ƙasa da ke Abuja, inda aka karrama ’yan Nijeriya sama da 400 da wasu baqi bakwai da yabo na ƙasa daban-daban.

“Za mu cigaba da kawar da duk wani nau’in ’yan bindiga, aikata laifuka, ta’addanci da tada ƙayar baya a ƙasar nan.

A cewar shugaban, karrama ’yan ƙasa ba ado ne kawai ba amma tunatarwa ne kan irin nauyin da ke kanau, yana mai cewa, “Dole ne a ko da yaushe mu yi ƙoƙarin yin iya ƙoƙarinmu ga ƙasarmu.”

Da ya ke bayyana taron a matsayin na ban girma da kishin ƙasa, Buhari ya ce, waɗanda aka karrama sun nuna bajinta wajen yi wa qasa hidima da kuma bil’adama, inda ya ce, ya karrama su ne kamar yadda dokar karramawa ta ƙasa CAP N43 ta dokokin Tarayyar Nijeriya ta tanada, 2004.

Buhari ya ƙara da cewa, tun da aka kafa gwamnatinsa, ba a samu wani kamfani na bayar da lambar yabo ta ƙasa kamar taron na ranar Laraba ba, “sai dai bikin na musamman da aka yi wa Cif MKO Abiola, Alhaji Baba Gana Kingibe da Cif Gani Fawehinmi.”

A cewarsa, an gudanar da bikin nasu ne musamman domin gyara kura-kuran da aka yi a baya, domin kwantar da hankulanmu da kuma yanke shawarar tsayawa tsayin daka a yanzu da kuma nan gaba domin tsarkake tsarin zaɓe da dimokuraɗiyyarmu.

Yayin da ya ke gabatar da cewa ’yan ƙasar da ke ba da gudummawar cigaban ƙasa sun cancanci ƙarfafawa da kuma a yaba musu, Buhari ya bayyana jin daɗinsa da cewa wasu daga cikin waɗanda aka karrama ba wai kawai suna yin alfahari da Nijeriya a fagen ƙasa ba ne, amma sun zama wata hanyar ƙarfafa wa matasan Nijeriya kwarin gwiwa ta hanyar aiki tuƙuru da sadaukarwa.