Na goyi bayan sayar da NNPC, inji El-Rufai

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce, Gwamnatin Nijeriya ta gaza a ɓangaren mai da iskar gas, don haka ya kamata ta janye kanta daga fannin.

El-Rufai ya ce, babu amfani gwamnati ta ci gaba da harkar mai, tunda duk abin da yi a ɓangaren, ciki har da cefanar da NNPC, haƙa ba ta cimma ruwa ba.

“Harafin L da aka ƙara a sunan NNPC babu abin da ya sauya; har yanzu kuɗaɗenmu suke ci, suna cewa, an samu riba, amma ba mu ga ko sisi ba.

“NNPC babbar matsala ce a Nijeriya, wadda dole mu magance ta, in ba haka ba za ta durƙusar da kasar nan,” inji shi, a A jawabinsa a Taron Zuba Jari na Kaduna (KADINVEST).

El-Rufai ya ce,  Don haka, “Babu dalilin gwamnati za ta ci gaba da yin harkar mai, ya kamata ta janye tunda ta gaza.”

Gwamnan ya ce, duk da cewa shgaban NNPC na yanzu, Mele Kyari yana yin iya ƙoƙarinsa, amma kamfanin ya gaza, kuma ya kamata a rufe shi.

Ya ce, vangarorin da ke bunƙasa a Nijeriya babu hannun gwamnati a cikinsu, kamar ɓangaren sadarwa da nishaɗi da sadarwa da sauransu.

Da ya ke jawabi kan taken taron, ‘Gina Tattalin Arziki Mai Nagarta’, El-Rufai ya ce, duk da matakan da aka ɗauka a NNPC, “Har yanzu da kuɗaɗen haraji ake gudanar da ƙasar nan.

“Dalili shi ne kuɗaɗen tallafin da NNPC ke biya sun laƙume abun da vangren mai ke samarwa, saboda haka ya kamata gwamnati ta sayar da kamfanin, ya janye kanta daga ɓangaren mai.

“Tun 1999 na ke wannan magana, lokacin ina shugabantar Hukumar Kula da Kamfanonin Gwamanti, kuma har yanzu ban canja matsayi ba.

“Sannan gwamnati ta cire kanta gaba ɗaya daga vangaren lantarki ta bar wa ’yan kasuwa ta koma gudanar da vangarorin, za ta samu kuɗaɗe.”