Nijeriya a matsayin ƙasar da ke fama da yunwa a duniya

Rahotanni daga Majalisar Ɗinkin Duniya sun nuna cewa sama da mutane miliyan 113 a faɗin ƙasashe 53 ne suka fuskanci matsananciyar yunwa a shekarar da ya gabata tare da rikici, annobar sauyin yanayi da kuma matsalolin tattalin arziki wanda ke haddasa rikicin abinci.

Aƙalla ’yan Nijeriya miliyan 25 ne ke fama da yunwa, yayin da mutane miliyan 9.3 ke fama da matsanancin ƙarancin abinci, dai-dai lokacin da ƙasar ke tsaka da fama da tashen-tashen hankula na masu ɗauke da makamai.

Nijeriya na fuskantar rikici daga kowane ɓangare, wanda ke ke daƙile hanyoyin cigaban ƙasar. Ba wai helkwatar talauci ta duniya ba ce kawai, har ma ta shiga cikin jerin ƙasashen da suka ɗaga tuta a matsayin wuraren da ake fama da yunwa a duniya. A wani rahoton haɗin gwiwa da hukumar samar da abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya (FAO) da hukumar samar da abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya suka fitar sun bayyana cewa, matsalar ƙarancin abinci ta ƙara tsananta a Nijeriya da wasu ƙasashe 18. Rahoton ya ƙara da cewa, ana sa ran adadin mutanen da ke fuskantar matsananciyar ƙarancin abinci a duniya zai cigaba da ƙaruwa a kullum. Daga cikin ƙasashen da ke fuskaantar wannan matsala bayan Nijeriya akwai Afghanistan, Habasha, Somaliya, Sudan ta Kudu, da Yemen. Kuma yawancin waɗannan ƙasashe sun gaza.

Darakta Janar na FAO, QU Dongyu, ya ƙara da cewa, tsananin fari da ake fama da shi a yankin kahon Afirka ya jefa mutane cikin halin yunwa, tare da lalata amfanin gona da kashe dabbobin da rayuwarsu ta dogara da su. “Mutanen da ke cikin ƙasashe mafi talauci musamman waɗanda har yanzu ba su murmure ba daga tasirin cutar ta COVID-19 suna fama da rikice-rikicen da ke faruwa ta fuskar ƙaruwar farashin kayan abinci da taki, gami da ɓacin yanayi.”

A cikin wani rahoto da ta fitar a shekarar da ta gabata, wata cibiyar bincike ta ƙasar Birtaniya mai suna Institute of Development Studies (IDS), ta sanya Nijeriya a matsayin ƙasa ta biyu mafi talauci a duniya da samun tsadar abinci. Ƙasa ta ɗaya ita ce Syria. Nijeriya ta kuma kasance cikin jerin ƙasashe 10 da suka fi fama da yunwa a cikin jerin ƙasashe masu fama da yunwa a duniya. Yankin da ya fi muni shi ne Arewa maso Gabas inda sama da mutane miliyan huɗu ke fuskantar barazanar ƙarancin abinci. Jihohin da suka fi muni su ne Adamawa, Borno da Yobe. Matsalar yunwa dai na ƙara ta’azzara ne sakamakon hauhawar farashin kayayyaki, musamman hauhawar farashin kayan masarufi wanda ya zuwa watan Agustan bana, ya kai shekaru 17 da ya kai kashi 20.5 bisa ɗari.

Matsalar rashin tsaro shi ne babban dalilin da ya haifar da yunwa. A matakin duniya, yaƙin da ke tsakanin Rasha da Yukren shi ne babban al’amari. Yukren dai ita ce babbar mai fitar da alkama. A Nijeriya, matsalar tsaron cikin gida ya haifar da yaƙi. A duk faɗin ƙasar, ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga sun sanya rayuwa ta yi wahala ga ‘yan ƙasa. Kullum suna garkuwa da mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba. An saki waɗanda suka yi sa’a bayan an biya ’yan ta’addam kuɗin fansa mai yawa. Waɗanda aka yi rashin sa’a kuma an kashe su. An kashe dubunnan mutane. Miliyoyin wasu kuma sun rasa matsugunansu inda su ke tsugune a sansanonin ’yan gudun hijira daban-daban.

A wasu sassan ƙasar kuma, makiyaya da ’yan ta’adda sukan kai hari kan manoma, lamarin da ya kori da yawa daga cikin manoman daga gonakinsu. A shekarar 2020 ne ‘yan ta’addar Boko Haram suka kai hari a wata gona a ƙauyen Zabarmari da ke ƙaramar hukumar Jere a jihar Borno, inda suka kashe ma’aikatan gona aƙalla 67. Ga wasu daga cikin waɗanda suka tsere daga harin ‘yan ta’addan, baƙin cikinsu shi ne lalata amfanin gonakinsu da shanu. A wurare irin su Zamfara ana tilastawa manoma da sauran mutanen ƙauye biyan haraji ga ’yan ta’addan domin a bar su zuwa gonakinsu. Babban dalilin wannan rashin tsaro shine rashin aikin yi. Wani ƙiyasi na masu ra’ayin rikau ya nuna cewa, yawan marasa aikin yi a Nijeriya ya haura kashi 33 cikin ɗari. Tun da yawancin matasa ba za su iya samun aikin yi ba, suna ƙirƙira wa kansu ɗaya a cikin masana’antar aikata laifuka. Noma, wanda zai iya zama alheri kuma ceto ga ƙasa, an yi watsi da shi saboda yawancin matasa ba sa son zuwa gonaki. Sun gwammace ayyukan farar kwala, waɗanda ba su da yawa a kwanakin nan. Rashin shugabanci shi ne tushen wazannan matsalolin. Tsawon shekaru, Nijeriya ba ta samu haziƙin shugaban da zai yi aiki ba dare ba rana wajen himma manyan manufofinmu ba. A halin yanzu dai ’yan Nijeriya da dama musamman matasa na ficewa daga ƙasar. Ƙwararrunmu, musamman likitoci, suna ƙaura zuwa ƙasashen waje don yin aiki saboda ba su samun isasshen kuɗi a gida. Cin hanci da rashawa ya zama ruwan dare kuma ya yi illa ga dukiyar ƙasa.

Ba zato ba tsammani, noma ya kasance babbar hanyar magance yunwa a Nijeriya. Don haka ya kamata gwamnatoci a kowane mataki su ƙarfafa gwiwar manoma ta hanyar samar musu da isasshen tsaro. Su kuma fito da tsare-tsare don magance matsalar abinci. A shekarar 2020, Majalisar Kula da Abinci ta Ƙasa ta amince da wani shiri na tsawon shekaru biyar don rage yunwa da rashin abinci mai gina jiki a Nijeriya. Shirin wanda zai gudana tsakanin shekarar 2021 zuwa 2025, ana sa ran zai rage yawan mutanen da ke fama da matsalar qarancin abinci mai gina jiki da kashi 50 cikin ɗari. Gwamnonin Nijeriya sun yi alƙawarin yin aiki domin ganin an aiwatar da wannan shiri.

Ya kamata gwamnati ta kuma yi la’akari da ba da ƙwarin gwiwa ga manoma. Muna da isasshen fili don noman abinci kuma dole ne mu yi wani abu don zamanantar da noma ta hanyar tura fasahar ƙere-ƙere. Ya kamata manoma su rungumi aikin injiniyoyi da kuma noma na zamani. Kamfanonin iri ya kamata su mai da hankali kan nau’ikan da aka ƙirƙira ta kwayoyin iri waɗanda za su inganta amfanin gona.

Mun yaba wa Bankin Raya Afirka (AfDB), wanda aka bayar da rahoton ya ƙaddamar da dala biliyan 1.5 na samar da abinci na gaggawa na Afirka don hana matsalar abinci da ke kunno kai. Muna kira ga sauran manyan ƙungiyoyi su kawo agaji ga ƙasashen da abin ya shafa.