Kada a bari ASUU ta sake shiga yajin aiki a ƙasar nan, kiran Gbajabiamila ga Gwamnati

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya a kan kada ta Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta sake shiga yajin aiki a ƙasar nan.

Gbajabiamila ya faɗi haka ne a martanin da ya yi ranar Juma’a dangane da janye yajin aiki na wata takwas da ASUU ta yi kwanan nan.

Ya ce har yanzu ba a warware matsalolin da ke tsakani ba, don haka ya buƙaci gwamnati da ƙungiyoyi da sauran ‘yan ƙasa da a soma tattaunawa kan makomar manyan makarantun gwamnatin ƙasar nan.

Ya ƙara da cewa, “Ina godiya ga takwarorina na Majalisar Wakilai na yanke shawarar shiga tsakani don samar da maslaha tsakanin Gwamnati da ASUU.

“Ina da ƙwarin gwiwar Majalisar za ta yi tsayin daka wajen tabbatar da Gwamnatin Tarayya ta ninka ƙoƙarinta ga ƙungiyar da kuma jami’o’i.

“Abin nadama ne aukuwar yajin aiki, kuma abin takaici ganin yadda yajin aikin ya yi tsayin da bai kamata ba,” inji shi.

By Editor