An buga littattafai huɗu dake bayyana yadda Xi Jinping ke aiki a ƙananan hukumomi

Daga CMG HAUSA

A kwanakin baya, aka buga wasu littattafai hudu dake bayyana yadda shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ke aiki a kananan hukumomi, ciki har da mai taken “A taimakawa jama’a kyautata zaman rayuwarsu yadda Xi Jinping ya yi aiki a Zhengding” da dai sauransu.

Littattafan guda huɗu, sun mayar da hankali ne kan yadda Xi Jinping ya jagoranta tare da inganta gyare-gyare a cikin gida da buɗe kofa ga ƙasashen waje da kuma zamanintar da ƙananan hukumomin da ya taɓa yi wa aiki. Kana an waiwayi yadda Xi Jinping yake gudanar da harkokin mulki tare da yadda yake mayar da hankali kan dukkan ɓangarori, da yadda yake da hangen nesa, da kulawa da zaman rayuwar jama’a, da tsare gaskiya da aiki tuƙuru, da jajircewa wajen yin ƙirƙire-ƙirƙire, da kuma sauke nauyin dake wuyansa.

Kazalika an yi cikakken bayani game da akidar Xi Jinping, da yadda yake mayar da hankali kan jama’a, da yanayin tunaninsa, da halinsa da kuma nasarar da ya cimma ta ban mamaki a ayyukansa.

Mai fassara: Bilkisu Xin