Ana sa ran yankin Hong Kong zai samu wani sabon cigaba a cikin shekaru biyar masu zuwa

Daga CMG HAUSA

Tun a lokacin babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta ƙasar Sin karo na 18, shugaban ƙasar Xi Jinping ya nuna kulawa matuka game da wadata da zaman lafiyar yankin musamman na Hong Kong, da moriyar jama’ar wurin da walwalarsu, inda ya yi nuni da cewa, ci gaba shi ne ginshikin raya yankin Hong Kong da kuma magance matsaloli daban-daban.

Shin ta yaya yankin Hong Kong zai samu sabon ci gaba cikin shekaru 5 masu zuwa?

A wajen bikin cika shekaru 25 da dawowar Hong Kong ƙasar Sin, da kuma bikin rantsar da gwamnati ta shida ta yankin, wanda aka gudanar a jiya Jumma’a, shugaba Xi Jinping ya gabatar da wasu dabaru 4 da yake fatan za su samar da ci gaban HK.

Dabarun huɗu sun haɗa da “Mayar da hankali kan ƙara matsayin shugabanci” da “Ƙara ƙarfin inganta ci gaba” da “Warware matsalolin da jama’a ke fuskanta “, da kuma “Wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali tare”.

Xi Jinping ya kuma bayyana fatan sabuwar gwamnatin yankin za ta aiwatar da manufar “ƙasa ɗaya, mai tsarin mulki biyu” tare da gudanar da ayyuka masu amfani, da kuma mai da hankali kan warware batutuwan da suka fi damun mazauna Hong Kong.

Xi Jinping ya bayyana cike da ƙauna cewa: “A halin yanzu, abin da ya fi jan hankulan jama’ar Hong Kong shi ne, fatan samun rayuwa mafi kyau, da zama a cikin gida mai fadi, da samun karin damammakin raya sana’o’i, da samar da ilimi mai inganci ga yara, da kuma samun kulawa mai inganci idan an tsufa.” Don haka, ya buƙaci sabuwar gwamnatin yankin da ta ɗauki buƙatar al’umma, musamman ma fararen hula, a matsayin babbar manufarta ta gudanar da mulki.

Bisa la’akari da yadda ake matukar buƙatar tsaro don samun ci gaba, shugaba Xi Jinping ya ce, bayan fuskantar tashin hankali, kowa yana jin cewa, Hong Kong ba zai kasance cikin rudani ba, kuma ba za a iya jinkirta ci gaban yankin ba. Yana mai cewa, dole ne a kawar da duk wani katsalandan tare da mai da hankali kan ci gabansa.”

Mai fassara: Bilkisu Xin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *