Hajji 2022: Malamai na ci gaba da ilimantar da mahajjatan Najeriya a Saudiyya

Daga MU’AZU HARDAWA a Madina

A ci gaba da ƙoƙarin ilimantar da mahajjata game da muhimmancin aikin Hajji kaɓaɓɓiya da take yi, Hukumar Hajji ta Najeriya (NAHCON) ta gargaɗi mahajjatan ƙasar da suka isa ƙasa mai tsarki don sauke farali kan su kasance masu lura da kuma bin doka yayin zamansu a Saudiyya.

Babban limamin Hukumar ‘Yan Sandan Najeriya, Sheikh Alhassan Yaakub, shi ne ya yi wannan gargaɗi a lokacin da yake gabatar da nasiha ga mahajjatan a birnin Madina.

Malamin ya buƙaci alhazan su gode wa Allah bisa baiwar da Ya yi musu ta zama daga masu sauke faralin Hajji a bana duk da dokoki da kuma ƙarancin kujeru da Gwamnatin Saudiyya ta bai wa Najeriya.

Daga nan, Sheikh Yaakub ya gabatar da malaman da Hukumar Hajji ta kawo don ilimantar da mahajjatan kan yadda za su gabatar da aikin Hajji karɓaɓɓe, wanda sakamakonsa shi Aljanna.

Yayin da ɗaya daga cikin malaman yake jawabi

Hajiya Khadija Gambo Hawaja daga Jihar Kaduna, na daga cikin tawagar malaman, ta bayyanawa mahajjatan muhimmancin ziyarar da ake kaiwa ga Manzon Allah (SAW) a Madina a lokacin Hajji. Ta kuma taɓo abin da ya shafi ɗaura niyya da shiga harami.

Taron ilimantarwar ya hori alhazan da su kasance masu nuna tausayi da kulawa a tsakaninsu, da kuma kiya dokokin Hajji da aka shimfiɗa.

Daga cikin malaman da suka halarci zaman akwai Barista Sulaiman Yusuf daga Jihar Edo da Imam Salisu Idris Oseni daga Juhar Edo, jami’an NAHCON da sauransu.