An ceto jaririn da aka sace a Asibitin Koyarwa na ATBU – Mahukunta

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar gudanarwar Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Ɓalewa da ke Bauchi (ATBUTH), ta ce ɗaya daga cikin tagwayen jarirai ‘yan kimanin makonni biyu da aka sace a asibitin an gano shi a Bauchi.

Dr. Haruna Liman, Shugaban Kwamitin Bada Shawarar Likitoci, CMAC, na asibitin ya bayyana haka, a lokacin da yake miƙa jaririn ga mahaifiyar ranar Talata a Bauchi.

Ya ce an sace jaririn daga hannun mahaifiyar a asibiti bayan kwana takwas da haihuwa.

“An sace jaririn ne a ranar 21 ga Satumba, 2022 da ƙarfe 4:30 na yamma daga hannun mahaifiyar da ke karɓar magani a asibiti.

“An ceto yaron a yau, 27 ga watan Satumba da misalin ƙarfe 1:00 na safe cikin ƙoshin lafiya da kwanciyar hankali.

“Muna godiya ga Allah da ƙoƙarin da jami’an tsaron cikin gida na asibitin, DSS, ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro suka yi wajen ceto jaririn,” inji shi.

Mista Liman ya ce tuni jami’an tsaro suka kama wata mata da ake zargi da kitsa wannan mugunyar aikin.

“A halin yanzu ana yi mata tambayoyi, abin da muka sani kenan bayan jami’an tsaro sun miƙa jaririn ga Hukumar Kula da Asibiti.

“Yanzu muna miqa ɗan tagwayen jaririn mako biyu ga mahaifiyar da iyalan cikin ƙoshin lafiya.

Shugaban ya bayyana cewa hukumar za ta yi nazari kan tsarin tsaro na asibitin tare da sanya ƙarin na’urorin fasahar tsaro a asibitin.

Hakimin Bauchi Nura Jumba, ya buƙaci mahukuntan asibitin da su sake duba tsarin tsaro na asibitin domin gujewa sake afkuwar irin haka.

Ya yi alƙawarin cewa a kodayaushe shugabannin gargajiya za su wayar da kan al’umma kan lokutan da suka dace na ziyartar marasa lafiya a asibiti.

Mista Jumba ya buƙaci hukumar da ta ƙulla alaƙa da iyali, da nufin ba su fahimtar juna.

Da yake mayar da martani a madadin iyalan jaririn, Shitu Kalid, ya bayyana jin daɗinsa ga mahukuntan asibitin bisa damuwar da suka nuna da kuma jami’an tsaro kan ceto jaririn.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *