An ceto waɗanda ake zargin an nemi maida su Kiristoci a Jos

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar tsaro ta DSS ta kai sumame wani gida da ke unguwar JMDB a yankin Tudun Wada da ke Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato, inda ta ceto mutum 21, ciki har da wasu almajirai.

Da take tabbatar da lamarin, Ƙungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI), ta shaida wa manema labarai cewa mutanen da aka kuɓutar sun ce an kai su cocin ne ta ƙarfin tsiya ana qoqarin mayar da su addinin Kiristanci.

Babban sakataren cocin ECWA, Rabaran Yunusa Nmadu, ya ce gidan da aka kai samamen na cocin ne, amma ba sa amfani da shi wajen canzawa mutanen addini da ƙarfin tuwo.

DSS dai ta kai samamen ne ranar 14 ga watan Yunin 2022, inda ta ceto mutanen da ake zargin an kawo su Jos ne daga wata jihar.

Kai samamen, a cewar Daraktan Agaji na JNI reshen Jihar ta Filato, kuma babban jami’in agaji na babban masallacin Juma’a na Jos, Xanjuma Khalid, ya zo ne bayan ɗaya daga cikin waɗanda aka ceto ɗin, Abdulrahman Usaini, wanda ya samu ya kuvuto ya yi zargin cewa an killace su a gidan tsawon watanni takwas.

Khalid ya ce DSS ta kai samamen ne bayan rahoton na JNI.

Ya ce lokacin da aka kai biyu daga cikin mutanen da aka ceto, Abdulrahman Usaini da Nura Usama ɗin hedikwatar DSS da ke Jos, aka damƙa su ga JNI, kawun Abdulrahman da malaminsu sun kasance ƙarƙashin kulawar DSS har sai da aka gano danginsu.

Abdulrahman, wanda ɗan asalin garin Azare ne a Jihar Bauchi, ya ce an kai shi garin Gombe ne don karatun Alƙur’ani, inda daga nan ne aka kai shi cocin ta ECWA da ke Jos.

Ya ce a watan Oktoban 2021, yana kan hanyar dawowa daga makarantar da ke unguwar Pantami, inda wasu suka kira shi ya wanke musu mota ƙirar Toyota Camry, inda suka ce wa masu motar dare ya yi, amma aka danna su cikinta ta ƙarfin tsiya.

“Sun kaimu cocin ECWA da ke Tumfure a Gombe, inda muka shafe mako uku a can. Bayan kwanakin, sai suka ce mana za a kai mu Jos.

“Wajen misalin ƙarfe 4:00 na safiyar ranar, muka ɗauki hanyar tafiya Jos. Zuwa ƙarfe 9:00 na safe mun kai hedikwatar cocin ECWA da ke Jos. Ban san Jos ba, wannan shi ne farkon zuwana.

“Mun buƙaci su mayar da mu Gombe saboda iyayenmu ba su san inda muke ba, amma suka ƙi.

“Bayan kwana ɗaya suka mayar da mu wani gida da ke Tudun Wada, inda muka shafe wata takwas a ciki. A iya tsawon wannan lokacin, sun riƙa koya mana ilimin addinin Kiristanci. Suna ba mu abinci da dukkan abubuwan da muke buƙata.

“Bayan mun shafe mako shida, sai aka kai mu cocin ECWA Good News da ke titin Ahmadu Bello don yin ibada a coci,” inji Abdulrahman.

Ya ce a ranar 13 ga watan Yunin 2022, ya sami damar tserewa bayan ya tsallake katangar gidan sannan ya gudu, yana neman agajin mutanen unguwar don ya samu komawa Azare a Jihar Bauchi.

Daga bisani aka kai shi wajen Shugaban Ƙungiyar Masu Sayar da Kabeji reshen kasuwar Farin Gada, Adamu Alhaji Adamu, wanda shi ma ɗan asalin Azaren ne.

Sai dai da yake tsokaci a kan batun, sakataren cocin ta ECWA, ya shaida wa manema labaru cewa waɗanda aka ceto daga gidan ba ta qarfin tsiya aka kai su ba, savanin yadda suka yi iƙirari.

Ya ce yana zargin cewa suna ƙoƙarin yin hakan ne don vata wa cocin suna, yana mai cewa cocinsu ba ta sauya wa mutane addini ta ƙarfin tsiya.

Ya ce: “Babu ƙamshin gaskiya a labarinsu. ECWA ƙungiya ce ta ƙasa da ƙasa, kuma tana ayyukan alheri da dama, kama daga na lafiya da wa’azi da kuma koya wa mutane sana’o’i.

“Gidan da aka kama su ana amfani da shi ne wajen taimaka wa mutane ba tare da la’akari da ƙabila ko addini ba. Wajen kamar makaranta ne, kuma dole sai wani ya kawo ka kafin mu karve ka.

“Ba ma karɓar ’yan ƙasa da shekara 18. Muna karɓar kuɗaɗe kafin mu karɓi mutum, muna koya musu sana’o’i na tsawon shekara ɗaya, kafin mu yaye su,” inji Rabaran Yunusa.

Da aka tambaye su ko DSS ta faɗa wa cocin cewa za ta kai samame gidan, Sakataren na ECWA ya ce, “su DSS ne ya kamata su amsa wannan tambayar. Watakila ba su san me ake yi a gidan ba, ka san kuma ba komai DSS za su faɗa maka ba.”