An damƙe ɗan sandan da ake zargi da karɓar na-goro a Edo

Daga BASHIR ISAH

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Edo ta damke jami’inta, Kwanstebul Victor Osabuohign, wanda aka yada bidiyonsa a kafafen sada zumunta yana karɓar cin hanci.

Mataimakiyar Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, ASP Jennifer Iwegbu ce ta ba da sanarwar hakan ranar Juma’a a Benin, babban birnin jihar.

An ga Osabuohign cikin wani bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta yana cinikin abin da za a ba shi a matsayin na-goro da wani matafiyi mai suna Arc. Bolu.

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya rawaito cewa, Iwegbu ta ce an kama jami’in da lamarin ya shafa kuma ana kan gudanar da bincike kan badaƙalar.

Ta ce rundunar ta kafa kwamitin bincike ƙarƙashin jagorancin ACP James Chu, domin binciko gaskiyar abin da ya wakana.

Daga nan, ta ce Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar, Mista Abutu Yaro, ya buƙaci al’ummar jihar da su rika kai rahoton duk dan sandan da aka gani ya aikata ba daidai ba don ɗaukar matakin da ya dace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *