Shugaban APC ya gargaɗi masu tayar da zaune tsaye a yankin Abia

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Adamu, ya bayyana baƙin cikinsa kan rashin haɗin kai a jam’iyyar reshen Jihar Abia, yana mai cewa rikicin ya fi na sauran jihohi ƙamari.

Adamu wanda ya yi magana a wani taro da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC na Abia a Abuja, ya caccaki tsohon ƙaramin ministan ma’adanai na ƙasa, Mista Uche Ogah, kan zarginsa da hannu a rikicin da ya ɓarke.

An ce ya nuna rashin jin daɗinsa da Ogah bisa zarginsa da jagorantar wata ƙungiyar da ke adawa da juna a cikin jam’iyyar APC ta jihar Abia, ko da bayan duk masu ruwa da tsaki sun sasanta ƙungiyoyin da ke rikici a wani taro a ranar 18 ga watan Yuni, 2022, a Ntalakwu Oboro a ƙaramar hukumar Ikwuano ta jihar.

Shugaban jam’iyyar kuma ya koka da cewa, ƙoƙarin da ake yi na haɗewar jam’iyyar APC a Abia ya ci tura, inda ya ƙara da cewa, a Abia ne ya sanya tsarin raba muƙamai na zaɓe da nufin daidaita ɓangarorin biyu da ke gaba da juna.

Adamu ya shawarci Ogah da ya saukar da kansa tare da haɗa kai da ɗan takarar gwamna a jam’iyyar APC a Abia, Ikechi Emenike, domin tabbatar da nasarar jam’iyyar a zaɓen 2023 mai zuwa.