Daga BASHIR ISAH
Akalla gawarwaki biyar ne aka gano yayin da wasu dama sun bace sakamakon hatsarin jirgin ruwan da ya auku ranar Litinin a yankin Karamar Hukumar Borgu a Jihar Neja.
Jami’in kula da iftila’i a yankin Borgu, Malam Musa Said, shi ne ya bayyana haka, inda ya ce a ci gaba da binciken da masu aikin ceto ke yi sun gano gawarwaki guda biyar, kuma ana ci gaba da neman ragowar mutanen da ba a gan su ba bayan aukuwar hatsarin.
Haka shi ma Shugaban Hukumar ba da Agajin Gaggawa na Jihar Neja, Abdullahi Baba Arah, ya tabbatar da aukuwar lamarin, tare da cewa har yanzu ba a tantance adadi na wadanda suka tsira da wadanda suka mutu ba a hatsarin ba.
Ya ce, jirgin mai dauke da fasinja 100 da sauran kayayyaki ya baro Dugga Mashaya a gundumar Dugga cikin Karamar Hukumar Borgu ne da nufin zuwa kasuwar Wara da ke Jihar Kebbi.
Ya kara da cewa, “NASEMA ta samu rahoto kan hatsarin jirgin ruwa da ya auku a Karamar Hukumar Borgu. Lamarin ya faru ne ranar Litinin, 15 ga Janairu 2024, da misalin karfe 2:05pm.”
MANHAJA ta ruwaito Jihar Neja ta yi fama da iftila’in hatsarin jirgin ruwa a tsakanin watannin baya-bayan nan wanda gwamnatin jihar ta ce tana yin bakin kokarinta wajen hana ci gaba da fuskantar hakan a fadin jihar.
