Cin zarafi a aure: Ina mafita (2)?

Spread the love

Tare da AMINA YUSUF ALI

Sannunku da jimirin karatun jaridarku mai farin jini ta Blueprint manhaja. Yau ma ga mu a wani makon mai albarka. A wannan makon muna tafe ne da bayani a kan yadda matan auren da suke fuskantar cin zarafi a gidan aure musamman a kasar Hausa.

Inda za ka ga cewa, mace ana cin zarafinta, ana hana ta abinci, da sauran hakkokinta na aure ga uwa uba kuma duka da wulakanci. Amma ta kafe ta haqura ta zauna a gidan. Me yake kawo hakan? Kuma meye mafita?

Yawanci sukan dauki matakin hadiye komai su cigaba da rayuwa a haka. Amma abin tambayar shi ne, anya hakan shi ne mafita? Idan ba shi ba ne mafita, to mecece sahihiyar mafitar? A makon da ya gabata mun warware muku zare har abawa kuma mun fara fede muku biri har wutsiya a wannan rubutun. Amma kafin a kammala lokaci y ayi halinsa.

Yanzu za mu cigaab da kawo muku dalilan da suke sa mata su zauna a gidajen auren da ake cin zarafinsu. Mun kawo muku dalilai hudu zuwa biyar a wancan makon yanzu kuma za mu ɗora. A sha karatu lafiya.

Dalili na biyar, akwai so. Hausawa sun ce, ‘so hana ganin laifi’. Tsakanin kuma mata da miji, sai Allah. Idan mace na son namiji duk irin cin zarafinta da zai ko ya tauye mata haqqi, tana iya shanyewa da kau da kai, tare da yi masa uzuri. Wata har dora ma kanta laifi take a zuciyarta don ta kare abin son nata.

Wata ko ta fusata ta tafi din, haka za ta haqura ta sake dawowa wajen masoyin nata, shi kuma ya cigaba daga inda ya tsaya a cin zarafinta. Ba ma idan ya iya ba ta hakuri da yin tausasan lafuzza ko ya iya yi mata wata kyauta a matsayin toshiyar baki. Duk lokacin da ya vata mata rai. Wata duk dukan da ya yi mata, in dai ya iya rarrashi, a take za ta yafe.

Na shida, akwai igiyar zato. Namiji yana azabtar da mace, amma kullum tana yi masa fatan zai gyara watarana. Wasu matan tsananin so ne yake rufe musu ido. Wasu kuma, hudubar magabata ce. Sai a ce, idan namiji yana cin zarafinki, to ki yi ta hakuri watarana sai labari. Amma kafin ki ba da labarin fa? Allah ya sa ma azaba ba ta kashe ki ba, da za ki ba da labarin.

Na bakwai, jahilci da rashin sanin mutuncin kai. Kawai ita gani take ta cancanci wannan cin zarafi da ake yi mata. Sannan tana da karancin ilimin gano hakkokinta.

Na takwas, akwai Raunannen tunani. Mutumin da yake cin zarafin mutane da ma yana da wani babban makami, wato raunana tunanin wanda yake cutarwar. Ya murde zancen ya nuna shi wanda ake cutarwar shi ne mai laifin. Haka wannan tunanin zai ta wanzuwa a zuciyar mace ya hana ta tavuka komai don fitar da kanta daga rayuwar cin zarafin.

Na tara, akwai rashin rashin samun kwarin gwiwa. Mace idan tana cikin rayuwar azaba ta gidan miji, ko da ta farga ta gano cewa, ta gudu kawai shi ne mafita, amma abin fa ba mai sauki ba ne. Sai ta yi ta sa rana. Daga karshe mata da dama ba sa cin nasara. {alilan Allah yake taimaka su iya cimma burinsu.

Na goma, sabo. Hausawa sun ce, sabo turken wawa. Mata da yawa suna kasa guduwa su bar gidajen auren da ake cuzguna musu saboda sabon da suka yi da gidan har ma da irin azabar da ake gana musu. Tsoron tafiya suke yi suna ganin ma idan sun yi gaba ma ba su san me za su tarar ba.

Na goma sha daya, akwai gado ko yanayin yadda ta taso. Ta saba da ganin ana cuzguna wa mata a danginsu. Don haka ita ma kawai ko dukanta miji yake yi, za ta ga ai ba laifi ba ne. Domin ba sabon abu ba ne. Ta saba da ganin haka wajen iyayenta ko yayye. Hasali ma dai ta dauka kowanne gidan aure haka ake zaman. Don haka, duk wuya ba wani hobbasa da za ta yi don ganin ta ceci kanta.

Na sha biyu, rashin sana’a da abin hannu. Matar da ba ta da abin hannunta takan dogara kacokan a kan mijinta. Idan aka yi rashin dace mijin nata na cikin rukunin wadancan mazajen masu azabtar da mata, to ta kade kuwa har ganyenta. Don ga azaba tana sha da wulakanci, wani zubin ma har da duka. Amma ba ta da yadda za ta fige ta gudu. Don ba ta da yadda za ta yi. Mai yiwuwa ba ta da iyaye ko ba su da karfi. Ga yara barkatai kun tara. Inda za ta ajiye yaran ma aiki ne, ballantana daukar nauyinsu. Hakan zai sa ta saduda ta hakura da dukkan azaba domin rashin madafa.

Na sha uku, tsoro. Wasu matan ba sa iya guduwa saboda tsoron abinda zai biyo baya. Wata tana jiye wa yaranta tsoro idan ta tafi ta bar su. Wata kuma har barazana yake mata cewa idan ta tafi ba za ta wanye lafiya ba. Hakan zai sa ta kasa tafiya.

Na sha hudu, rashin sanin makoma. Wata za ta yi ta tunanin anya idan ta bar shi za ta iya rayuwa ba shi? Anya za ta iya son wani ko wani ya so ta bayan shi? Ko kuma wa zai aure ta da tulin ‘ya’yanta?

Na sha biyar, ki- fadi. Wata tana tunanin Kada ta fita daga gidan miji wasu su ga gazawarta su yi mata dariya. Musamman makiya ko dangin miji ko kishiya ko tsohon saurayi ko wani daban. Sai ka ga ta zauna ta shanye cin zarafi, duka da wulakanci.

To ina mafita?

Ya kamata mahukunta da gwamnati da malamai da shugabanni a cikin al’umma su tsaya su tsawatar. A dena cin zarafi da wulakanta mata a gidan aure. Ya kamata al’umma a hada kai a kan duk wanda yake cuzguna wa mata a dinga hana shi muqami ko wani auren idan ya so kari.

Sannan iyaye su dinga sauraren ‘ya’yansu mata da ke gidan aure su saita musu matsaloli. Ba wai kawai daga ta kawo karar miji a ce ta koma ta yi hakuri ba. Hakurin ba shi da amfani idan ba za a zauna a duba matsalar ba.

Yin haka yana nuna wa miji kuna neman kai da ita. Kuma zai cigaba da muzguna mata. Kuma gudun da kuke kada ta dawo, da wuya dai ba a yi sakin ba. Domin aure ba zai tafi ba kwanciyar hankali da fahimtar juna.

Kuma wani lokacin rashin saurarenta din zai sa ta daina gaya wa kowa. Kuma hakan zai gadar mata da ciwon damuwa (depression.)

Don Allah ku tsaya mata. Idan ma ya kama a hada da hukuma, ku wuce mata gaba. Ba a ce su kashe mata aure ba. Amma aqalla a gyara matsalar kada ta zama babba yadda shi zai iya cutar da ita ko ita ta kai bango ta yanke mummunan hukunci.

Sannan kuma sai al’umma sun daina kyama da zargi da dora laifi ga zawarawa laifi sannan mata za su mike su nema wa kansu ‘yanci.

Ku ma mata mu nemi sana’a kuma mu rage haihuwa barkatai.

Irin wadannan mata, Babbar hanyar da za ka bi don shawo kansu shi ne, a zauna da su, a tattauna a fahimci matslolinsu. Sannan a warware. ba kullum fa mace ke da laifi ba. An san akwai matan da da za a biye musu sai su mai da aure ba ibada ba. A dai kara dubawa.

Mu hadu a mako mai zuwa idan Allah ya kai rai.

By Editor