An garƙame makusantan Bello Turji a gidan kaso na Kuje

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Ankama mutane huɗu da ake zargi da kasancewa masu alaƙa da fitaccen shugaban ƴan ta’adda, Bello Turji, a gidan yarin Kuje bisa umarnin Mai Shari’a Emeka Nwite na babbar kotun tarayya da ke Abuja. Waɗanda ake zargin sun haɗa da Musa Muhammad Kamarawa, Abubakar Hashimu (wanda aka fi sani da “Doctor”), Samuel Chinedu, da Lucky Chukwuma.

Sun musanta zargin da ake musu bayan an karanta musu tuhume-tuhume 11 da ake yi musu a kotu. Mai Shari’a Nwite ya ɗage shari’ar zuwa ranar 10 ga Fabrairu don ci gaba da sauraren shari’ar.

A cikin tuhume-tuhumen, ana zargin waɗanda ake tuhuma da bayar da tallafi ga ƙungiyoyin ƴan ta’adda tsakanin shekarar 2018 zuwa 2022 a jihohin Sokoto, Zamfara da Kaduna.

Tallafin da ake zargin sun haɗa da kayan abinci, magunguna, kayan soja da na ƴan sanda, da kayan gine-gine kamar siminti, roba, da sikelin ƙarfe. Haka kuma, ana zargin wasu daga cikinsu da sayo bindiga daga ƙasar Libya domin bayarwa ga wani ɗan ta’adda da ake kira Kachalla Halilu, wanda aka biya Naira miliyan 28.5.

Bello Turji da wasu mutum uku da ake zargi su ma suna cikin jerin waɗanda ake nema ruwa a jallo, inda su ka haɗa da Bashir Abdullahi, Aminu Muhammad, da Sani Lawal.

Lauyan gwamnati, David Kaswe, ya bayyana cewa gwamnati tana kan gudanar da bincike don gano inda suke. Mai Shari’a Nwite ya amince da canza sunayensu zuwa “ruwa a jallo” bayan babu wani ƙorafi daga lauyoyin da ke kare sauran waɗanda ake tuhuma.

A lokacin zaman kotu, lauyoyin da ke kare wasu daga cikin waɗanda ake zargin sun yi ƙoƙarin ƙalubalantar hurumin kotun don sauraron shari’ar. Sai dai Mai Shari’a Nwite ya ba da umarnin a fara karanta tuhume-tuhumen ga waɗanda aka kama a hannun hukuma. Bayan an karanta tuhume-tuhumen da Hausa da Turanci, waɗanda ake zargin sun musanta laifukan da ake tuhumarsu da su, sannan kotu ta yi alƙawarin sauraron buƙatar beli idan har sun shirya.

By ukarofi