Gwamnatin Kano za ta cigaba da inganta harkar Lafiya a jihar – Gwamna Abba

Spread the love

Daga RABIU SANUSI a Kano

A ƙoƙarin kare rayukan ƙananan yara da aka haifa a jihar Kano, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya dawo da ayyukan rigakafi na yau da kullum, waɗanda aka yi watsi da su na tsawon watanni 18 a ƙarƙashin tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje ba tare da wata hujja ba.

Kakakin Gwamna Abba Kabir Yusuf, Malam Sanusi Bature Dawakin Tofa da ya fitar da sanarwar ga manema Labarai.

Rahotanni sun bayyana cewa daga farkon wa’adinsa a 2023, Gwamna Yusuf ya bada fifiko ga lafiyar mata da yara tare da nuna matuƙar damuwa kan dakatar da shirye-shiryen rigakafin da tsohuwar gwamnatin Gandujen ta yi watsi da shi.

Bature ya ce gwamnan ya bada umarnin a gaggauta dawo da waɗannan muhimman ayyuka tare da bada tabbacin samar da kuɗaɗe ga aikin rigakafin a matakin jiha da tarayya.

A Lokacin ƙaddamar da kashi na biyu na makon lafiyar mata da jarirai na shekarar 2024, Gwamna Abba ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na rage mace-macen mata da ƙananan yara.

Sanarwar ta bayyana cewa abin da kasafin kuɗin jihar Kano na 2024 ya ƙunsa, ya haɗa da samar da ƙwaƙƙwaran tanadi na ayyukan rigakafi da tabbatar da ɗorewar shirin da kuma fatan isar sa ga dukkan mazaunin jihar.

By Babaji