Gwamna Fintiri ya samar da sababbin sarakuna da masarautu a Adamawa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Gwamnan Adamawa, Umaru Fintiri ya sanar da ƙirƙiro sabbin sarakuna da masarautu guda shida a jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a gidan gwamnatin jihar dake Yola wanda wani ɓangare na ayyukan ƙarshen shekara.

Masarautun sune; Hoba, wato Hong mai daraja ta biyu; Madagali (Gulak mai daraja ta biyu); Michika (Michika, daraja ta biyu); Fufore (Fufore daraja ta biyu); Gombi (Gombi, daraja ta uku); Maiha (Maiha, daraja ta uku); Yungur (Dumne, daraja ta uku),” kamar yadda gwamnan ya wallafa a shafin X ranar Litinin.

Ya ce gyare-gyaren za su taimaka wajen inganta harkokin gwamnati da ƙarfafa masarautun gargajiya don amfanin jihar da al’ummarta.

Ya ƙara da cewa masarautun gargajiya suna matuƙar taka muhimmiyar rawa wajen samar da zaman lafiya acikin al’umma don haka ne halin tsaro ya ke cigaba da inganta a jihar.

By Babaji