Tare da BASHIR MUDI YAKASAI
Dokoki da ƙulle–ƙulle da Turawan Birtaniya da ƙawayenta, Amurkawa da Faransawa Turawan Portugal da na Italiya da kuma dukkan Turawan Yamma da Gabas, waɗanda suka kitsa mulkin mallaka a ƙasashen Afrika, dokoki ne da suka yi wa wannan ƙasa ta Nijeriya da baibayi da takunkumi da kuma ɗaurin talata afukar tattalin arziƙi da siyasa da kuma zamantakewa ba tare da warware su ba.
Aka shiga kaɗa kuge da karya gangar mutuwa da kuma busa ƙahonhuna na ‘yan farauta da sunan ‘Yyan siyasa masu kishin ƙasa irin su mista Herbert Macaulay da jam’iyyarsa ta NNDP da Dakta Nmandi Azkuwe da Jam’iyyar Cif Obafemi Awolowo ta “Egbe Omo Oduwa” (ƙungiyar Jikokin Oduduwa), wacce ta rikiɗe da halin taƙiya ta koma AG. Mu ma nan Arewa mun zo da jam’iyyar Mutanen Arewa, wacce ta koma NPC, a ƙarƙashin jagorancin Sir.Ahmadu Bello, Sardaunan Sokoto. Shi ma Malam Aminu Kano ya shiga Jam’iyyar Sawaba, Wato NEPU.
’Yan takarda (wato ’yan boko) da ’yan dandi, (wato scholars) na yau da jiya da dubban ɗaliban su da suka yaye daga Jami’o’i da makarantun ilimi da na fasaha da kimiyya sama da 300 su zauna a warware dukkan ƙulle–ƙullen da aka yi a shekara ta 1922 da suka ba wa Turawan Birtaniya da ’yan kanzaginsu damar kwasar dukiyar ƙasa kamar kuza da azurfa da tagulla da tama da kuma zinariya a lardunan Jos da Kano da Zariya da Bauchi da kuma Benuwe.
Daga shekara ta 1912 zuwa shekara ta 1963 kamfanoni fiye da 110 sun shiga kwasar wannan ganima, wanda mutane sama 50,000 suke yi musu aiki ba tare da biyan su ba, sai dai kuɗin fince, wanda ba su wuce sama da kashi ɗaya cikin 100 (1%) ba na abin da suke samu. Haka abubuwan suke tafiya har wannan lokaci – 2023.
Ma’adanai da kuma makamashi na Najeriya dukiyoyi ne da ake da su a Najeriya, amma masu alfarmasu sune Turawan Yamma da Amurka, yanzu kuma ƙabilun Asiya sun kunno kai suna ta wadaƙarsu,. ba mai hana su, saboda ’yan takarda da ’yan dandi sun ƙi wayar da kan gwamnati yadda za a yi wa waɗannan Turawan Yamma da na Amurka. Yanzu da Turawan Gabas mai nisa, Rasha da Chana, wato Sin suna ta kawo mana bara. Idan muka faɗa tarkonsu, to, babu shakka babu ranar fita su ma.
Karya ce tsagoranta bayan sun tungume mu da sarari da sarƙoƙi sai suka jefa mu rijiya gaba dubu, suka kawo karnuka da suka horar, suka wanke musu ƙwaƙwale, saboda haka ba su tunani na sun a kansu da jama’arsa sai na birnin London, ko Paris kuma Washinton D.C, amma talauci da fatara da kuma rashin tabbas ga ɗan Nijeriya ya sa tsohon Shugaban ƙasa, Cif Olusegun Obasanjo (1999–2007) ya furta cewa, an tafka babban kuskure da muka zaɓi mulkin Dimukraɗiyya a wannan ƙasa. Wannan somi-somi ga abin da muke buƙata na ba mu yarda ba, a dawo da baƙon nan, domin kuwa ya sha ƙwai.
Bari mu dawo kan hanya ta yin bayani na gaske, domin kuwa “an bar kari tun ran tubani”, ba a ba mu ’yanci sai suka bar mu da ɗaurin talala, mu na zaton a sake muke ashe a ɗaure muke tamau, domin ba inda za mu sai birnin London ko Paris ko kuma biranan Washinton D.C da na New York, sai abin da suka tsara mana shine daidai, wanda shi ribarsu ce a kullum, mu kuma tafka asara muke yi: Ta kai ta kawo ’yan Naijeriya kashi 85 cikin 100 suna kwana cikin yunwa.
Muna da ma’adanai sun fi kala 100 da duniya ke buƙata ga kuma makamashi kamar shi man fetur da Gas da sauran dangoginsa, ga kuma ‘wind energy’ (albarkatun iska) na kusan awa 24.
Nijeriya na da mugudanan ruwa da za su ba mu wutar lantarki duk tsahon shekara, amma saboda sakacin ’yan takardar ƙasar nan, wato ‘elite’, kamar yadda muka ce da takwarorinsu ‘scholars’ masu ilimi su wanda ya tabbatar mana da cewa, jakuna ɗauke da kayan littattafa.
Rashin fito da wannan ƙarara shi ya sa ƙasannan take cikin wannan rayuwa ta ƙaƙa-na-ka-yi, kamar zaman birni ne, kamar yadda bBafulatanin daji da ya zo birni ya lura a garin babu misissika, kuma babu rumbu ya ce “da alama ana zaman ƙarya a wannan garin.”
Tun da Nijeriya ba ta da iko da dukiyar ƙasarta, wannan yana bayar da tabbacin ana zaman ƙarya, don haka kuwa za a sha wahala ta yunwa da fatara da kuma rashin zaman lafiya. Mu sani duniya gabaɗayanta sauya ba ta da wani buri illa tattalin arzikinta da suke kira ‘GNP’, wato, ‘Gross National Product’ – kasafin da ƙasa ta tanada.
Duk duniya ’yan takardarsu (elites) babu wani abu a gabansu illah tattalin arzikin ƙasashensu, haka masu iliminsu (scholars), wato gungun mutanen da suke da ikon su faɗa-a-ji, saboda ƙarfinsu na jama’a suke bin su kuma idanuwarsu a rufe, kuma sun san duk wani tuggu na siyasa, na zamantakewa da kuma kuɗaɗe masu kauri tare da su. Bayan haka suna da ’yan baranda masu yawa tare da su, wato makaɗa da maraya da kuma mawaƙa tare da su. Ga kuma malaman jami’a waɗanda sunayensu na haƙiƙa suke ɗauke da alamar nan da ke cewa shi ko ita mai ilimi, wato dakta, kamar Dakta B ko C har zuwa Z, ko kuma sunan yana ɗauke da ‘Farfesa’ Bala ko ‘Farsefa’ Tanko ko kuma ‘Farfesa’ Delu da dai sauransu.
Saboda haka Nijeriya tun lokacin da aka ƙuƙƙulla kuma aka kakkafa tarakunan mulkin mallaka, aka kuma horar da ’yan takarda (elites) da kuma ’yan baranda (scholars) da suke kora talakawa kamar dabbobi babu wani mayar da hankali ko alƙibla (focus) kan wani al’amari da zai kuɓutar da talakawan Nijeriya daga turakun da aka turke mu tun shekara ta 1922, ga shi an bi mu da takunkumi, ba mu da ikon mu faɗa aji ga dabaibayina hana mu zuwa ko ki na sai iyaka gurin da suka ƙayyade duk da cewa ɗaurin talalar da suka yi mana muna ganin a sake muke tun shekara ta 1960.
Sun ƙyanƙyashe dubbai ko ma na ce miliyoyin ɓeraye da gafiyoyi da kuma tururuwoyi, waɗanda suke jidar dukiyar ƙasa ta hanyoyi fiye da takun masaki. Idan ka na so ka tabbatar da wannan magana je ka ka yi hira da shugabannin EFCC da ta Shugaban Efcc a lokacin mulkin Goodluck Jonathan da kuma wanda ya ce ta Ibrahim Lamorɗe ko kuma ka tuntuɓi na yanzu ka sha labari.
Nijeriya na buƙatar mutane irin su Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu da mataimakinsa Kashim Shattima Mustapha da falsafassu ta mulki na ’no going back’, wato duk abin da suka ɗauko ba su ba koma wa baya, kullum a tafe suke, idan suka zo da ƙulli ba ka fahinta ba, to, a zauna a tattaunawa (dialogue) a fito da gaskiyar magana da kuma manufarta.
Fatanmu kafin wa’adinsu Bola da Shettima ya ƙare a shekara ta 2031 (wataƙila) an warware dukkan matsalolin da aka tsara su ta fuskar tsarin mulkin dimukraɗiyya. Amma maganar gaskiya, Nijeriya da sauran ƙasashen Afrika da aka yi musu mulkin mallaka, kuma ake iƙirarin an ba su ’yanci wannan ƙarya ce tsagwaranta.
Warware waɗannan matsaloli da suka sha kawunan su ne;
Na farko duk ƙasashen Afrika su haɗe kawunansu su rabu da karɓar duk wata shawara, kowacce iri ce daga ƙasashen Turai, Turan na Yamma ne ko na Gabas. Haka duk wata shawara daga Amurka, komai kyanta, a saka ta a kwandon shara, kuma a bi ta da ƙasa a rufe, saboda mun sami ilimi na juyi da sauyi, kamar yadda duniya take jujjuyawa ba a tsaye take ba guri guda ba.
Wajibi ne mu kalli Nijeriya da ’yan Nijeriya kaɗai, kuma duk abin da zai biyo baya, sai Nijeriya kawai kafin mu je ga wani shashe na Afrika ballantana na wata nahiya ta duniya.
Bari mu kwana nan kafin mu zo da wasu batutuwa mako mai zuwa, idan Allah ya kai mu.
