Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano
Danmakwayon Kano kuma Sakataren Masarautar Kano, Hakimin Dawakin Kudu, Alhaji Yusuf Kabir, ya gargaɗi masu riƙe da sarautar gargajiya da su rungumi ɗabi’ar zaman lafiya da al’ummarsu domin samar da cigaba mai ɗorewa a yankunansu.
Ya yi wannan gargaɗi ne a lokacin da yake naɗa wasu sabbin masu sarautar gargajiya da wani mai unguwa a fadarsa da ke Dawakin Kudu, a ranar Lahadin da ta gabata.
Waɗanda aka naɗa sun haɗa da Yunusa Magaji a matsayin Sarkin Askar Dawakin Kudu, Idris Aminu a matsayin Sarkin Noman Dawakin Kudu, da Hamza Ado Abdullahi a matsayin Mai Unguwar Garin Durawa.
Alhaji Yusuf Kabir ya bayyana cewa zaman lafiya shi ne ginshiƙin cigaban kowace al’umma, yana mai jaddada cewa soyayya, haɗin kai da kula da jin daɗin jama’a su ne manyan abubuwan da ya kamata sabbin masu sarautar su sanya a gaba. Ya yi musu fatan alheri da nasara a sabbin muƙamansu.
Da yake jawabi a madadin sauran waɗanda aka naɗa, Sarkin Noman Dawakin Kudu, Idris Aminu, ya bayyana ranar a matsayin wata rana mai tarihi a rayuwarsa, yana mai nuna farin ciki da godiya ga Allah bisa wannan dama. Ya tabbatar wa Hakimin Dawakin Kudu cewa za su zauna lafiya da al’umma tare da gudanar da mulki bisa gaskiya da adalci.
Ya kuma yi kira ga al’umma da su mara musu baya da addu’a, tare da basu shawarwari masu amfani domin samun damar sauke nauyin da Allah Ya ɗora musu, tare da bunƙasa yankin gaba ɗaya.
