Dalibi ya kashe kansa bayan an cinye shi N600,000 a cacar ƙwallon ƙafa

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Ana zargin wani ɗalibi ya rataye kansa har lahira saboda an cinye masa Naira 600,000 a wurin cacar ƙwallon kafa.

ɗalibin da ke aji uku a fannin Kimiyar Kwamfuta a Jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida da ke Lapai a Jihar Neja, an gano gawarsa ne a safiyar ranar Litinin.

Shaidu sun ce ajiyar kuɗin aka ba wa mamacin, amma ya buga cacar ƙwallon ƙafa da su, aka cinye shi.

Majiyoyi sun bayyana cewa wani makwabcinsa ne ya tsinci gawar a rataye a jikin fankar ɗakinsa, inda aka sanar da hukumomi game da lamarin.

Wani dalibi a jami’ar ya shaida wa wakilimu cewa, “Gaskiya ne wani abokin karatunmu ya rataye kansa saboda an cinye kudin hayar da aka ba shi ajiya, a inda ya buga caca da kuɗin.”

Shugaban ƙungiyar ɗalibai (SUG) ta Jami’ar, Aliyu Abubakar, ya tabbatar da faruwar lamarin wanda ya bayyana a matsayin abin takaici.

Kakakin ’yan sanda na Jihar Neja, SP Wasiu Abidoun ya shaida wa wakilinmu cewa, da safiyar ranar Litinin suka samu labarin tsintar gawar dalibin mai suna Kelɓin Danlami, bayan ya rataye kansa a jikin fankar sama a ɗakinsa.

“Wani ɗalibi makwabcinsa da ya gano halin da ake ciki ne ya ankarar da mutane aka garzaya da shi Babban Asibitin Lapai, inda likitoci suka tabbatar ya mutu.

“’Yan sanda na gudanr da bincike domin gano haƙiƙanin abin da ya faru, kuma sun tuntuɓi iyayen mamacin,” a cewar SP Abiodun.

By ukarofi