An gurfanar da wasu mutum biyu a gaban wata Kotun Majistare mai zamanta a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo, kan zargin wulaƙanta wata gawa.
Kamfanin Dillancincin Labarai na Nijeriya (NAN), ya rawaito ana tuhumar mutum biyun ne da aka gurfanar ranar Juma’a da haɗin baki wajen wulaƙanta gawar ta hanyar jefar da ita a wani shago.
Sai dai babu wani cikakken bayani kan yadda aka yi aka kai gawar shagon, da kuma ko sun aikata mata wani rashin ɗa’a.
Lauyar mai tuhuma, ASP Foluke Adedosu, ta shaida wa kotun cewa, an aiktata laifin ne ran 12 ga Satumba, laifin da ta ce ya saɓa wa sassa na 516 da 242(1)(b) na Kundin Dokokin Manyan Laifuka na Jihar Oyo, na 2000.
Sai dai masu kare kansu sun musanta zargin da ake yi musu.
Tuni dai Alƙalin kotun, Mai Shari’a O. A Enilolobo, ta ba da belin waɗanda ake tuhumar kan N100,000 ga kowannensu da kuma shaida dai-ɗaya.
Kotu ta ɗage shari’ar zuwa ranar 21 ga Fabrairu mai zuwa.
