An kafa hukumar KSCHMA don taimakekeniyar lafiya ga ɗaukacin al’ummar Kano – Dr Rahila

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano

An bayyana cewa an kafa Hukumar Taimakekeniyar Lafiya ne domin amfanin daukacin al’ummar Jihar Kano, ba wai ma’aikata kawai ba.

Hukumar ta KSCHMA an kafata ne don taimakekeniyar kula da lafiyar ma’aikatan gwamnati da kamfanoni da ma daukacin al’umma ba lallai sai ma’aikacin gwamnati ba.

Hukumar ta taimakekiniyar lafiya kowa zai iya yin rajista domin kula da lafiyarsa da ta iyalinsa gwargwardon yadda doka da yarjejeniyar wannan hukuma ta tanada na kula da lafiyar al’umma ta hanyar taimakekeniya.

Wannan bayani ya fito ne daga bakin Shugabar hukumar ta Jihar Kano Dr Rahila Mukhtar inda ta tabbatar da cewa wannan hukumar tana tsaye tsarin daka wajen samar da ingantaccen lafiya ga duk mazauna jihar Kano.

A karshe ta yi kira ga daukacin al’umma da su tabbatar sun shiga tsarin kuma su tabbartar iyali, dangi da abokan arziki su ma sun yi rajista wanda za su samu kulawa a kulum a kowane lokaci dare da rana daga hukumar KSCHMA.

By Editor