Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Wasu da ba a san ko su wane ne ba sun kai hari Cibiyar Kula Da Tsaro Ta Kuje da bama-bamai a daren ranar Talata.
Majiyoyi sun ce, ana ci gaba da harbe-harbe da ƙarar fashewar abubuwa a kusa da wurin, wanda ke wani yanki da ake kira Shetuko a ƙaramar hukumar Kuje.
Har zuwa lokacin da ake wannan rahoto, ba a tabbatar da ainihin musabbabin faruwar lamarin ba, amma majiyoyin da ke kusa da wurin sun ce wataƙila harin ta’addanci ne.
Da aka tuntuɓi Mataimakin Sufeto Janar na ’yan sanda (AIG), shiyya ta 7 a Abuja, Aliyu Ndatsu, ya shaida wa manema labarai cewa, zai zanta da jama’a idan suka gama gudanar da bincike.