Daga LUBABATU LEI
Xiaozhong Johnny wani mai wallafa bidiyo ne a shafin sada zumunta, wanda ya dan yi suna a ƙasar Sin. Xiaozhong ya fara zuwa Afirka ne sama da shekaru biyu da suka wuce, kafin daga bisani ya zauna a birnin Lome, babban birnin ƙasar Togo.
Kamar yadda matasan yanzu suke yi, Xiaozhong shi ma ya kan dauki hotunan bidiyo iri na “Vlog” bisa ga harkokin rayuwarsa na yau da kullum a Afirka, sa’an nan ya wallafa su a shafukan sada zumunta bisa sunan Xiaozhong Johnny, sai dai bai yi zaton hakan zai sa ya samu dimbin masu bibiyarsa ba.
Cikin shekarun biyu da suka wuce, Xiaozhong ya ziyarci kasashen Afirka 13, tare da wallafa hotunan bidiyo sama da 300, lamarin da ya sa ya samu masu bibiyarsa kusan miliyan a shafukan sada zumunta.
Wasu sun ce sun yi farin ciki da samun damar bin sawun Xiaozhong ziyartar ƙasashen Afirka ba tare da fita daga gida ba. Waɗannan hotunan bidiyo da Xiaozhong ya wallafa, sun kuma sa masu bibiyarsa sun samu damar ƙara fahimtar haƙiƙanin yanayin da ake ciki a Afirka daga dukkan fannoni, musamman ma sun taimaka wajen gyara wasu kura-kuran da a baya suka samu wajen fahimtar nahiyar.
Xiaozhong ya ce, “Na je Cote d’Ivoire, na je Gabon, kuma ta hoton bidiyon da na wallafa, masu bibiyarmu sun gano cewa, lallai akwai hanyoyi da gine-gine masu kyau a wurin, kuma al’umma na jin dadin rayuwarsu, sun kuma tambaye ni, da gaske nan Afirka ne? Ina ganin bidiyon da na wallafa sun kawo gyara ga ra’ayoyinsu.”
Ya zuwa ƙarshen bara, shekaru 12 a jere ne ƙasar Sin ta kasance ta farko wajen yawan yin ciniki da ƙasashen Afirka, baya ga haka, Afirka ta zama ta biyu ga ƙasar Sin wajen yawan samar da kwangilar gine-gine.
Dimbin ayyukan more rayuwa da ƙasar Sin ta aiwatar a ƙasashen Afirka, sun taimaka wajen inganta yanayin ayyukan more rayuwa, da ma rayuwar al’ummar ƙasashen. Daga cikin masu bibiyar malam Xiaozhong, akwai wasu da ke kiran shi “manzon Sin da Afirka”.
Hakika abun haka yake, a yayin da hulɗar tattalin arziki da ciniki ke kara ƙarfafa a tsakanin Sin da Afirka, al’ummar sassan biyu ma na ƙara cuɗanya da juna, bisa ga taimakon da irinsu Xiaozhong suka bayar, al’ummar sassan biyu na ƙara fahimtar juna da kuma amincewa da juna.
A haƙiƙa, irinsu Xiaozhong da ke rayuwa a Afirka, tare da wallafa bidiyo game da rayuwarsu a Afirka suna da yawa, kuma ta bidiyon da suke wallafawa, ƙarin Sinawa na samun damar fahimtar al’ummar ƙasashen Afirka, da al’adunsu, da bunƙasar tattalin arziki, da zaman al’umma na ƙasashen, baya ga kuma yadda hakan ya taimaka wajen haɗa zukatansu, duk da nisan da ke tsakaninsu da ma bambancin al’adunsu.
Amma abun baƙin ciki shi ne, akwai ‘yan tsirarun mutane da suka ɗauki hotunan bidiyon da ba su dace ba, tare da wallafa su a shafukan sada zumunta. Ga misali a kwanan baya, an kama wani dan ƙasar Sin da ke rayuwa a Malawi, wanda ya wallafa bidiyon da ake ganin yana nuna ƙabilanci.
A game da lamarin, bi da bi, ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin, da ma ofishin jakadancin ƙasar da ke Malawi, sun yi Allah wadai da abun da ya yi, kuma shugaban sashen kula da harkokin Afirka na ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Mr. Wu Peng, shi ma ya bayyana cewa, har kullum ƙasar Sin na nuna rashin amincewa da nuna ƙabilanci, kana kasar za ta ci gaba da daƙile abubuwan da ke baza ra’ayin ƙabilanci a shafukan sada zumunta.
A game da lamarin, ya kamata mu gane cewa, a duk ƙasashe da shiyyoyi, akwai mutane masu kirki da ma marasa kirki, amma marasa kirki ‘yan tsiraru ne, waɗanda ba sa wakiltar wata kasa, ko al’ummarta baki ɗaya ba.
Sin da ƙasashen Afirka na da daɗaɗɗen zumunci, kuma nasarorin da aka cimma bisa haɗin gwiwar sassan biyu ta fannoni daban daban ba su da sauƙi, don haka, ya kamata mu darajanta su. “Kada dai mu bari wake ɗaya ya ɓata miya”, balle ma a ce a bari wasu su yi amfani da waken wajen cimma yunƙurinsa na musamman.
