Daga BASHIR ISAH
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya yi wa majalisarsa garambawul a ranar Laraba yayin da ya rage wata bakwai kafin zaɓen 2023.
Kazalika, Shugaban ya rantsar da sabbin ministoci guda bakwai waɗanda Majalisar Dattawa ta amince da naɗinsu kwanan nan.
Bayan rantsar da su, Buhari ya yi kira ga sabbin ministocin da su ɗauki wannan muƙami da suka samu a matsayin wata dama ta yi wa ƙasa aiki bilhaƙƙi.
Sabbin ministocin da aka rantsar ɗin sun haɗa da; Henry Ikoh (Abia), Umana Okon Umana (Akwa-Ibom), Udi Odum (Ribas), Ademola Adegoroye (Ondo), Umar Ibrahim El-Yakub (Kano), Goodluck Nana Opiah (Imo) da kuma Ekumankama Nkama (Ebonyi).
Ministocin na mazaunin maye gurbi ne ga ministocin da suka ajiye aiki don shiga takarar zaɓen 2023.
Bikin rantsawar ya guna ne a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja kuma kafin taron Majalisar Zartarwa, inda aka yi tsit na miniti ɗaya don jimami da kuma martaba ruhin Sakatare-Janar na OPEC, Mohammed Barkindo wanda Allah Yayi masa cikawa a Talatar da ta gabata.
