An kama ɗan sandan bogi mai alaƙanta kan sa da CSP a Kano

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta cafke wani mutum mai suna Adamu Musa, mai shekaru 35, mazaunin Kureken Sani, bisa zargin yin sojan gona a matsayin babban jami’in ’yan sanda da kuma damfarar jama’a.

Rundunar ta ce an kama wanda ake zargin ne a ranar 1 ga Satumba 2026, da misalin ƙarfe 7:30 na dare, bayan samun rahoto da bayanan sirri daga Sashen ’Yan Sandan Panshekara.

A cewar sanarwar da Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar ranar Talata, Adamu Musa ya kasance yana gabatar da kansa a matsayin CSP, inda yake yaudarar mutane da cewa yana da tasiri wajen samo musu guraben aikin ’yan sanda da kuma sauya wuraren aiki.

Rundunar ta ce wanda ake zargin ya riƙa amfani da hotunan bogi da aka gyara, da kuma hotunan da aka samar ta hanyar fasahar AI, inda aka haɗa hotonsa da na manyan jami’an ’Yan Sandan Nijeriya domin ya ba damfararsa sahihanci.

Binciken farko ya nuna cewa ya yi amfani da waɗannan hotuna tare da sunayen wasu manyan jami’an ’yan sanda wajen yaudarar mutane, yana karɓar kuɗi da sunan zai taimaka musu wajen samun aikin ’yan sanda ko kuma sauya wuraren aikinsu.

A yayin binciken gidan wanda ake zargin, jami’an tsaro sun gano wasu kayayyaki da suka haɗa da riga da wando na kayan aikin ’yan sanda guda ɗaya, takalman baƙi guda biyu, kayan camouflage guda ɗaya, rigar uniform mai shuɗi guda ɗaya, da kuma tsabar kuɗi Naira 300,000.

Rundunar ta ce Adamu Musa yana hannun jami’an tsaro, kuma za a gurfanar da shi a gaban kotu bayan kammala bincike.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kuma gargadi jama’a da su yi taka-tsantsan da masu damfara da masu kwaikwayon jami’an tsaro, musamman waɗanda ke amfani da fasahar gyaran hoto da AI wajen ƙirƙirar hotunan bogi domin yaudarar jama’a da karɓar kuɗi.

By ukarofi